Yadda ake dambun nama
Dambun nama nau’in sarrafa nama da ake yi a Arewacin Nijeriya. Ana iya yin dambun nama da kalolin nama kamarsu: naman rago, naman akuya ko kuma naman kaza da sauran dangogin nama. Ana ajiye dambun nama domin tarairayar mai gida, ko kuma saukar baƙi na musamman.
Abubuwan Da Ake Buƙata
[gyara sashe | gyara masomin]1. Nama
2. Kayan ƙamshi
3. Kori
4. Thyme
5. Sinadarin ɗanɗano
6. Yaji haɗaɗɗe
7. Albasa da tafarnuwa
Yadda Ake Haɗawa
[gyara sashe | gyara masomin]1. Da farko za a sami nama, a yanke wajen da babu kitse sai a wanke nama ya fita tas.
2. A cikin tukunya babba a zuba wannan nama da wadataccen ruwa, sai a zuba su albasa, kayan ƙamshi, kori, thyme da ɗan sinadarin ɗanɗano.
3. A bar naman ya dahu sosai, har sai naman ya fara dagargajewa….in ruwa ya kusa ƙarewa sai a ƙara ruwa domin ya isa dafa naman.
4. Cikin turmi mai tsafta a zuba nama a daka har sai ya daku.
Daga Hafsat_Shettimah: Wasu daga wannan gaɓar suke zuba mai a cikin tukunya, su yi ta juyawa, har sai naman ya soyu amma ni ga yadda nake nawa.
[gyara sashe | gyara masomin]5. A zuba wadataccen mai cikin tukunya mai zurfi, sai a zuba wannan dakakken nama, a yi ta juyawa da muciya, har sai nama ya fara yin ja, sai a ɗebo wannan yaji a zuba. A nan za a sake jin ƙamshin ya tashi sosai.
6. A wannan lokaci naman ya kusa sauka, sai a kula da wajen juyawa domin kar nama ya soyu da yawa ko ya ƙone. A kula wurin juyin, domin in an bar shi zai ƙone.
7. A sami kalanda mai kyau, da tukunya sai a juye sai a bar shi har sai man jiki ya tsane tas da kansa [1]
- ↑ Yadda Ake Dambun Nama (wikihausa.com.ng)