Yargoje
Appearance
Ƴargoje ƙauye ne dake a karamar hukumar Kankara a jihar Katsina, Nijeriya.
Mafi yawanci mutanen dake garin yargoje manoma ne da makiyaya. Yargoje nada yawan yan boko wanda suka rike mukamai a bangarori da dama a jihar katsina da baki dayan Nigeria, Garine ne da ke dauke da dazukka masu cike da albarkatun cikin kasa da kasar noma mai inganci. Kasuwar yargoje na daya daga manyan kasuwanannin jihar katsina wadda ke ci duk ranar asabar. Mutanen yargoje mutane ne masu karamci ga baki da yan cikin gida.[1]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Hadiza Sanusi Yargoje