Yaudara

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Yaudara: wata abu ce mara daɗi kuma mara ƙyau, yaudara ta kasance abu mai ɗaci ga wanda aka yiwa kuma abu ce da addinai ba su yarda da ita ba kuma suka yi hani da ayi ta, yaudara dai a yanzun ta zama ruwan dare domin zamu iya cewa kowane ɓangare yanzun yaudara ta ɓulla duk da ba abu bace mai kyau.

Asali ita yaudara dai anfi sanin tane a tsakanin masoya inda takan haifar da matsaloli da dama ga masoyin da aka yaudara walau mace ko namiji, to amman yanzun zamu iya cewa duk wata hulda ta mutum da mutum walau wacce ake iya gani ko akasin haka to yaudara takan iya shigowa ciki.

Inda akafi yin yaudara[gyara sashe | gyara masomin]

  • A wajen soyayya
  • Wajen kasuwanci
  • Wajen karatu

Da dai sauran su

Abinda yaudara ke haifarwa[gyara sashe | gyara masomin]

Akwai abubuwa da dama da yaudara kan haifar musamman ga wanda aka yaudara saboda takaici da kuma ɗacin abinda aka masa.

  • Bugun zuciya
  • Lalacewar kasuwanci
  • Rashin lafiya mai tsanani

Da dai sauran su[1]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]