Yawon gudu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Yawon gudu a bikin aure

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

A rana ta farko akan fara da yawon gudu ne a inda amarya da sauran ƙawaye zasu fita domin zuwa yawon gudu. Sukanyi ta wannan yawon gudun har zuwa la'asar, sannan su dawo gida su wuce zuwa gidan ɓoyo. Da daddare kuma akan matan gidan ango da amaryar da nono ko turare, akan biya kuɗin buɗe ƙofa kafin ƙawayen amarya su buɗe ƙofar. Da an shiga wannan dakin za'a fesa ma amarya wannan turaren ko nono daganan kuma wannan tsohuwar zata goyata domin kaita gidan ƙunshi, ita kuma amarya da sauran ƙawaye su cigaba da kuka da kururuwa na juyayin rabuwa.[1]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://www.academia.edu/39248587/AURE_DA_ZAMANTAKEWA_DAGA_FARKO_ZUWA_KARSHE_A_MAHANGAR_ZAMANI_DA_MUSULUNCI