Yendi
Yendi | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Ghana | ||||
Yankuna na Ghana | Yankin Arewaci | ||||
Gundumomin Ghana | Yendi Municipal District | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 51,339 (2020) | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Altitude (en) | 155 m |
Yendi gari ne, kuma shine babban birnin gundumar Yendi Municipal a yankin Arewacin Ghana.[1] A shekarar 2012 yawan mutanen Yendi ya kai mutane 52,008.[2] A cikin garin Yendi Sarkin Dagbon, yake zama, masarautar itace masarautar Ghana mafi dadewa.
Tattalin Arziki a garin
[gyara sashe | gyara masomin]Mutanen Yendi galibi manoma ne masu noma hatsi musamman masara, masarar Guinea da gero. Haka kuma suna shuka tubas, irin su doya dankali da sauran su. Yendi cibiyar kasuwanci ce kamar yadda aka kafa ta a tsakiyar mafi yawan garuruwa/kauyuka a gaɓar arewaci. Yawancin mutanen da ke tafiya zuwa Tamale da kuma bayan titin Gabas dole ne su bi ta Yendi wannan ne ya mai da ita muhimmiyar tashar sufuri.
Al'adun Garin
[gyara sashe | gyara masomin]Yendi waje ne mai muhimmanci da al-adu iri - iri saboda itace masarautar Sarkin Dagbon inda yake zaune a masarautar. Shi Yaa yana zaune ne a Yendi inda nan ne masarautar shi take.
Ma'adinai
[gyara sashe | gyara masomin]A shekarar 2004, shawarwari sun kuma bayyana don haɗa ma'adinan ƙarfe a cikin kewayen Yendi ta hanyar dogo.
duba Sheini Hills
Garuruwa da Birane a cikin Yendi da kewaye
[gyara sashe | gyara masomin]Duba wannan maɓallin bulu ɗin,Garuruwa da ƙauyuka a ciki da wajen Yendi a cikin babban birni na Yendi
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Northern » Yendi Municipal district Archived ga Maris, 5, 2013 at the Wayback Machine
- ↑ "World Gazetteer online". World-gazetteer.com. Archived from the original on September 30, 2007.