Jump to content

Zama da Maɗaukin Ƙanwa Zumunci

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Zama Da Maɗaukin Kanwa; Zumunci

[gyara sashe | gyara masomin]

Wannan muƙala cigaban zango na farko ne akan Al'adar zumunci a wajen Bahaushe.

Bahaushe, da kuma musulmi.

A inda suturarsu da harshensu ba su ɗauke su da muhimmanci ba.Kai har da addini, al’ada da tunani, babu wani abu muhimmi, sai wanda Bature ya yi, ko ya faɗ. Ga masu irin wannan tunani na Nasara, maganarsu, rayuwarsu da tunaninsu duk na Bature ne. Farko dai, matarsu 1, Ƴaƴa 2-3. Ga baƙar rowa kamar yaro ɗan yaye, ƙin zumunci kamar ɗan tsako. Kare yafi ɗan uwa, Farkarsa tafi matar aure. Ya san tarihin turai, bai san danginsa ba ko na ƙasarsa.

Ƙyale dala’ ilu ka ɗauki jarida. Jikinka na Kano zuciyarka a London, Shi da maƙwabcinsa kuwa ba ruwan wani da wani(mahaukaci ya yi baƙo), Jikinka baƙi zuciya ta Nasara. To wannan shi ne baƙin Bature, ɗan boko ne, ko ba ɗan boko ba. Waɗanan hujjoji tare da wasu da bamu kawo su ba, su ne suka gurgunta al’adun Bahaushe musamman ta fuskar zumunci.

Matakin Farko Na Lalata Zumunci

[gyara sashe | gyara masomin]

1- Bai Kirani ba, bazan kira shi ba. 2- Bai neme ni ba, saboda me zan nemeshi. 3- Bai yi mani magana ba, don me zanyi masa magana. 4- Bai zuwa wurina, saboda me zanje wurinsa ba

Jama'a rayuwa bata da tabbas, sai da uzuri da ƙaunar juna na zahiri da kuma ɓoye.

Zuwan ilmin boko ƙasar Hausa ya yi tasiri a kan rayuwar Bahaushe ta yau da kullum ta fuskoki da yawa. Ilmin boko ya zo tare da wasu sababbin al’amura da ada basu a al’adun Bahaushe.To amma saboda rungumar da Bahaushe ya yiwa ilmin boko, sai aka samu wasu al’adun da Bahaushe ya gada kaka da kakanni ko dai sun ɓace gaba ɗaya, ko kuma sun samu gurɓata.

Da farko dai ilmin boko, Nasara ya zo da shi a in da shi dai mai bin addinin kirista ne. Watau almasihu wanda ba ya wuce mace ɗaya, watau a tsarin iyalansa ba ya wuce namiji ya auri mata ɗaya da ƴan ƴaƴansu.

Wannan kuwa ya saɓa da tsarin iyalin Bahaushe don a gida zaka samu kaka namiji da mace, sannan za ka samu uba da uwa da ƴaƴansu. A wani lokaci ma akan samu ƴaƴan ƴan uwa da ƙanne da barori da dai sauransu. Rungumar da wasu Hausawa masu iƙirari ilimin boko suka yi wa tsarin iyali Turawa shi ya sa suka nesanta da ƴan uwansu. Wanda yake shi ma wani reshe ne da ke raunana lamarin zumunci a al’ummar Hausawa.

Bayan ga wannan, ilimin boko ya haifar da aikin gwamnati a inda wannan aiki kan Sanƴa mutum zuwa wani gari na daban daga na haihuwarsa, sannan kuma wanda ya samu aikin gwamnati zai iya kasancewa ya koma unguwar Turawa da ake kira (GRA) nan ma ya sanya ya yinisa da ƴan uwansa sai dai in wani sha’ani ya samu, sannan ya je ko kuma ƴan uwa su zo.

Wannan rayuwa ta ilmin boko ta sauya abubuwa masu tarin yawa, musamman wajen ziyara ko halartar wani sha’ani da ya shafi ‘yan uwa, kamar gaisuwar rasuwa ta’aziyya ko suna ko bikin aure. Domin ko dai ya yi wa ƴan uwa nisa, ko kuma ba shi da lokaci. Bisa dalilin cewa duk wani ma’aikacin gwamnati ba shi da wata rana ta shi ta kansa in ban da Asabar da Lahadi.Wannan ya sanya gudanar da harkar zumunci ta yi matuƙar wuya. Bugu da ƙari wannan rayuwa ta Turawa da mafi yawan masu ilmin boko suka ɗauka ta ƙara durƙusar da harkar zumunci. Don kuwa shi Bature ya na da wata al’ada,da a ke cewa “ daga ni, sai ɗa na”, wanda ya yi kama da wata karin magana mai cewa: “daga ƙwauri sai gwiwa”. Wannan ɗabi’a kuwa ta saɓa da ta Bahaushe nesa ba kusa ba, saboda shi Bahaushe ya gaji rungumar juna da tallafawa. Duk wanda ya gaji rungumar juna da tallafawa, duk wanda ya shiga wani hali, shin na kusa ne, ko na nesa? (ɗan uwa ko bare).

Tabbas rayuwar Bahaushe ta sauya ƙwarai, saboda ta ɗauki wani sabon salo ta sanadiyyar yawaitar Hausawa masu ilmin boko, ko kuma masu ra’ayin boko. Ma’ana waɗanda suka rungumi al’adun Bature suka manta da al’adun Bahaushe. Misali idan aka dubi haƙƙin maƙwabtaka da aka san Hausawa na tsarawa a da, a yanzu ya yi rauni.

Gudun zumunci da ƙyamar dangi; Duk wanda ya faɗa irin wannan rayuwa, yakan koma baƙin Bature. Haka kuma yakan koma yana ƙyamar wani ya kusance shi, daga shi sai matarsa da ƴaƴansa, ko karensa, idan ma har akwai ƴaƴan ke nan. Wannan ne ya haifar da ƙin riƙon ƴaƴan ƴan uwa ko ziyartar dangi watau zumunta.

Tsarin muhalli a yanzu ya ɗauki wa tashi na rayuwa Turawa. Wato ba akan haɗa katanga. Kowa gidansa a kulle, sai a shekara maƙwabci bai sa maƙwabcinsa a ido ba. Ballantana a yi zumunci yawa ta sanadiyyar yin watsi da al’adun da aka gada iyaye da kakanin. A da Bahauhse ya na da hanyoyin ƙara ƙulla zumunci da yawan gaske, kamar auren zumunci, halartar sha’anin ƴan uwa kamar bikin suna, da bikin aure,da zaman makoki na mutuwa, sa rana. Kai har in an zo yiwa yaro kaciya, sai an taro ƴan uwa dangin uwa da na uba. Sannan kuma shi kansa wannan taron na kaciya ya na ƙara ƙulla zumunci, ba kawai a tsakanin ƴan’ uwan yaron ba, hatta a tsakanin tsararrakin yaron, waɗanda aka yiwa kaciya tare. Don kuwa wannan zumunci kan ɗore har girma, har a wasu lokuta ma akan yi misali da cewa ai wane amini na ne, saboda kuwa tare aka yi mana kaciya, yanzu kuwa sai a asibiti,ake yiwa yara kaciya sha-ka-tafi.

Shi ma auren zumunci ya taimaka sosai ta wajen ƙara ƙulla zumunci. Bahaushe kan aurar da ɗansa ko ƴarsa ga wanda duk ya ga ya dace sa kuma ƴaƴan, saboda ladabi da biyayya da al’ada ta tanada ba ɗan zai ƙi yarda da hukuncin iyaye.

To amma fa yanzu da aka samu watsuwar ilmin boko a ƙasar Hausa, to sai fa kawai wayewar kai ta nuna wa Ƴar boko cewar ai auren zumunci auren takura ne. Don kuwa ba a bani yarinya ta zaɓi wanda take so sannan kuma ƴaƴan sai suka nuna suna da Ƴanci, don haka ba dole ne iyaye su zaɓar masu abokan aure ba. Haka sai a bar su su zaɓi wanda suka ga dama wai kawai don ƴanci.

Wannan ya samu goyan baya ne ta sanadin yawaita ƴan boko da kuma yawaita karance- karancen littaffan Turawa, da kallace -kallacen majigi. Haka kuma ana samun ƙungiyoyi sa- kai da ke samun tallafi daga ƙasashen Turai don cusa wa jama’a ra’ayi da su yi watsi da ala’adunsu. Su kuma dage wurin kare ƴancinsu daga juna mai kare yancin yara. Domin har wani parfaganda (progaganda) ake yi da ake cewa, wai a daina yiwa yara aure da wuri don yana kawo ciwon yankan gishiri.

Ko kuma su ce auren dole shi kuma yana kawo karuwanci, wannan kuwa duk ya faru ne, saboda watsuwar ilmin boko da kuma al’adun Bature. Bugu da ƙari duk wanɗannan abubuwa da sun yi wa harkar zumunci dabaibayi don gaba ɗaya zumunci Bahaushe ya sanya guru ba kamar yadda aka san shi da farko ba.

Duk da irin sababbin al’adu, sannan kuma baƙi game da harkar zumunci, akwai masu kyau da kuma marasa kyau. Idan muka tsaya muka yi nazarin wasu kyawawan sababbin al’adu kuma baƙi,waɗanda ilmin boko ya zo da su, sai mu ce lallai sun taimaka matuƙa da gaske wajen ƙara ƙulla zumunta ta wata fuskar. Kamar haɗa abota sanadiyar zaman aji tare zaman ma’aikata, yi wa ƙasa hidima (bautar ƙasa NYSC) tare da zuwan ilmin boko ne ya kawo haɗa abota ka mu ce zumunci, saboda yin makaranta ɗaya ko kuma aji ɗaya kamar ƴan gari ɗaya a firamare, sai kuma ƴan gari daban- daban, ko kuma wata jiha watau a sakandare, ko kwaleji, ko jami’a. Wannan zumunci kan ɗore har girma kuma har Ƴaƴa da jikoki.

Sannan kuma ilmin boko ya haifar da aikin gwamnati, a inda zaka sannan haɗa ma’aikata daga wurare daban-daban a ma’aikata, ko kamfani ɗaya, sai ka samu zumunci ya yi ƙarfi sosai. Haka kuma, sakamakon karatun boko in aka ƙare na jami’a, ko kwalejin kimiyya da fasha, sai mutum (Ɗalibi) a tura shi wata jiha ta daban, saboda ya yi wa ƙasarsa hidima.

To a irin wannan haɗuwa ma akan ƙulla zumunci mai ƙarfin gaske, saboda ko da an gama, watau an rabu sai ka samu wannan zumunci ya ɗore har Ƴaƴa da jikoki.

YANAYIN TATTALIN ARZIKI(TALAUCI)

[gyara sashe | gyara masomin]

Harkar zumunci ta samu naƙasu a sanadiyyar yanayin tattalin arziki, da ya koma baya, don kuma ya kawo ƙarancin kyaututtuka, da rage ziyarce-ziyarce, da ɗaukar nauyi. Bisa ga yadda yanayin tattalin arziki ke da mahimmanci ga rayuwa ta yau da kullum. Zumunci ya samu tasarin haka ne, musamman in muka duba yadda al’umma suka takura ta sadiyyar haka. Bisa wannan,sai aka samu faruwar rowa, ko maƙe hannu, ma’ana an samu ƙarancin kyaututtuka da sukan wakana a tsakanin ƴan uwa. Waɗannan suka haɗa da gudunmowar sha’ani, kamar bikin aure, ko suna, ko kuma kyauta ta ƙara ƙulla zumunci da dai Sauransu.

Wannan kuwa ya faru ne, saboda ko da mutum na son ya yi alherin to abin bai isa a ce ya bayar ba. Bayan wannan kuma,sai wani tasirin da ake samu,ta fuskar yanayin tattalin arziki ta yadda zumunci ya naƙasa.

A sanadin yanke shi, saboda rage ziyarce-ziyarcen ƴan’uwa kusa ko na nesa. wannan kuma ya faru ne saboda tsawaltar kuɗin mota. Ko kuma ɗan abin da akan riƙe don a yiwa ƴan uwa tsaraba. Haka kuma su waɗanda za’a ziyarta ɗin su ma suna fama da kansu. Don haka sai ka samu ƴan uwa sun daɗe ba su ga juna ba, amma kuma babu mai laifi, don kuwa ya zama dole ne, sannan kuma gidan kowa da shi. Bugu da ƙari, akwai wani sashi da yanayin tattalin arziki ya yiwa zumunci cikas,shi ne, kuma wajen da ƴan’uwa kan ɗauki yara, ko ƴaƴan juna, don riƙo ko goyo, a da, sai dai ka samu wa, ko ƙani ya ɗauki ɗan Ɗan’uwa da nufin riƙe shi tun ƙuruciya har girma, ya aurar da shi,ga ciyarwa, da shayarwa, da tufatarwa, kai da duk abi da uban yakan yiwa ɗan cikin sa, sai yayi masa ba tare da nuna damuwa ba. Amma yanzu abun ya fuskara sai ɗai-ɗai, saboda haka halin da ake ciki.

Bisa ga haƙiƙanin gaskiya zumunci ya samu tawaya, saboda ko da mutum na son yin alheri ga ɗan uwansa to a yanzu babu hali. Sannan kuma gashi yanzu son abin duniya ya zurme a zukata mutane, mai ba su abin hannunsa shi ne mutum. A yau in kana da abin hannunka to ka kai ne karami a gida, sai ka koma kai ne babba, don kawai ka na da abin bayarwa.

A ƙarshe in muka duba irin durƙushewar da zumunci ya yi, babu ko tambaba ya auku ne, saboda karayar tattalin arziki da ya shafi dukkan wani mahaluki.To ashe kuwa dole ne ya shafi zumunci kai har ma al’ada gaba ɗaya,wasu.abubuwan bisa tilas akan haƙura.

INA MAFITA?

[gyara sashe | gyara masomin]

Matuƙar aka rutsa mage a cikin ɗaki, to dole ta nemi mafita inda zata gudu, don ta tsira da ranta, ta samu ta kuɓuta. Bisa wannan dalili, ina mai ba da shawarwara tare da yin kira ga dukkan Bahaushe da Bahaushiya, da cewa mu farka daga barcin da muke yi, mu san kanmu, mu kula da kanmu, da mu tsare kanmu. Mu kama zumunci da kyau, kuma da gaske, kar a yi mana sakiyar da ba ruwa. Dukkan mai hankali ya kamata ya dawo cikin hayyancinsa ya tsaya ya yi wa rayuwarsa kallon natsuwa. Watau kallo irin na sayen goron tsohuwa. Wajibi ne mu sanya kishin harshenmu, da al’adunmu da addininmu, saboda su ne rayuwar mutum gaba ɗaya. Matuƙar aka ce mutum ya rasa su, to zai yi ballagazar rayuwa mara manufa da amfani. Domin ya yi ɗigirgire, ko kan-tafi da rayuwarsa,an kuwa ce “kan-tafi masomin asara” .

A ƙarshe wannan muƙala ta ɗan taɓo, wasu daga cikin al’amura da suka shafi zumunci tun daga ma’anarsa,da matsayinsa,da nau’o’insa,da kuma dalilan dakan samar da shi. Yanayinsa a zamanin da kuma matsayinsa a wannan zamani, tare da matsalolin da yake fuskanta.

Tabbas su waɗannan matsaloli su ne suka Sanƴa harkar zumuncin Bahaushe ya taɓarɓare ta fuskoki da dama. Idan aka dube su ta mahanga al’ada,da addinin musulunci, da kuma a hankalce sun saɓa wa al’adu, da addinin Bahaushe.

Idan kuma muka kalli waɗannan ɗabi’u, sai muce sun saɓa wa hankali. Wannan muƙala ta fito da wasu kaɗan daga cikin fa’idojin zumunci ta fuskar al’ada da kuma addini. An bayyana baƙin ɗabi’un waɗanda Bahaushe ya ara daga wasu baƙin al’ummu, tare da nuna irin muninsu,da nauyinsu, da matsayinsu a mizanin al’adar Bahaushe. Bisa dalilin aibinsu da illolin da suka haifar wa Bahaushe yasa ake ƙyamarsu. Domin a zamanin da ba a san Bahaushe da su ba,shi yasa na kawo shawarwari ta yadda za a magance matsalolin.

Mun riga mun ji irin illolin da waɗannan baƙin ɗabi’un suka yi, ko suke yi,ko kuma zasu yi mana. Ta fuskoki marasa iyaka, kuma ta kusurwoyi daban daban. Domin haka,ina fatan wannan muƙala, ta zama kamar matashiya ce ga masu hankali daga cikinmu maza da mata. Allah Ya tsare mu Ya bamu ikon gyarawa amin. Assalamu alaikum.

Askalani I. H(1988) Bulugul Marami. Darul Fikr Beirut Lebanon.

Dakta. Mu'azu Muhammad Sa'adu Kudan Kan Yaro Kundi (Dutse) Shugaban Sashen Harsunan Najeriya Sule Lamiɗo University Kafin Hausa.

Annawawi I.(2005)Riyadus Salihin. Darul Fikr Beirut Lebanon Bargery, G. F. (1993) A Hausa-English Dictionary and English-Hausa Vocabulary Ahmadu Bello University Zaria.

Adam M. T(1997)Asalin Hausawa da Harshen su, Kano Nigeria.

Ɗangambo, A. (1980) “Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa”, Triumph Kano.

ENCARTA (2009), English Dictionary Microsoft Corporation Softwire.

Gummi A.M(1980) Alƙur'ani mai girma,Tarjamar Hausa. Hadimil Haramaini sharifaini Makka. Gummi A(1980)Fassarar Hadisai Arba'in.Northern Nigerian Publication. Co.

Hornby.A.S(2006) Oxford Advanced Learner’s Dictionary University Press New York. 

Imam A.(1937)Magana Jari ce .Northern Nigeria Publication Company Zaria.

Imam A.(1939)Ruwan bagaja Northern Nigeria Publication Company Zaria.

Jabiru A.(1958) Na gari na kowa.Northern Nigeria Publication Company Zaria.

Kudan.M.S(1997)“Zumuncin Bahaushe”kundin Digirina (B.A.Hausa) Usman Ɗanfodiyo University, Sokoto.

Kudan M.S(2008) “Hauka A Idon Bahaushe” kundin Digiri na (M.A.Hausa) Usman Ɗanfodiyo University, Sokoto.

Kudan M.S( 2010) Ƙuruciya a Al’adar Bahaushe AlBashir Printing Press Kaduna.

Kudan M.S( 2012) Baƙin Bature (Baƙin Mutum Da Kan Banasare)Wanda a ka Gabatar A Kwalejin Koyon Larabci Da Addini Musulunci Ta Shabab Dake Unguwar Dosa Kaduna.

Kudan M.S.( 2013)Ballagazar Uwa Wanda a ka Gabatar A Kwalejin Koyon Larabci Da Addini Musulunci Ta Shabab Dake Unguwar Dosa Kaduna.

Malik I.(1970)Muwaɗɗa Malik. Darul Fikr Beirut Lebanon.

Magaji Ɗan Dabo Kudan.(2005)Hira da shi a gidansa Tattibu ƙofar Arewa, Kudan. Madauci I.(1963)Al'adun Hausawa Northern Nigeria Publication Company, Zaria.

Rashid H.(1995)Kingship in Hausa.Seminer Paper ,Bayero University Kano.

Sadiya G.Y.(2005)Talauci Hauka ne ?Super Print Press.

Sarki H.A.(2000)Zuwan Musulunci a Afirka da shigowarsa ƙasar Hausa.

G.A. Computer Centre.Ikere – Ekiti, Ekiti State.

Suyuɗi A.(Babu shekarar bugawa) Jami'ul Hadis. Darul Fikr Beirut Lebanon.

Skinner (1999) ƙamus na Turanci da Hausa. Northern Nigeria Publication Company, Zaria.

Wali U.A.(1990)Hausa Kingship Term.M.A.Hausa Jami’ar Bayero Kano.