Jump to content

Zamantakewar Iyali

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Zamantakewar iyali a kasar hausa wani ƙayataccen al'amari ne. Tarihi ya nuna cewa, Hausawa suna zamantakewar rayuwa ne da ake kira “Gandu” (polygamous family) iyali da ya ƙunshi: kakanni, iyaye, ƴaƴa da kuma jikoki a waje guda. Agola shine Wanda ke zaune da mamanshi a gidan aurenta kuma mijin maman nashi ba shi yahaifeshi ba. [1].

Jerin Sunayen Iyali a Kasar Hausa[gyara sashe | gyara masomin]

Hausawa na da sunaye na musamman da ake yiwa ko wani mutum dake gandu ko iyali kaman haka:

Kaka: Mahaifi ko Mahaifiyar Uba ko Uwa a gida ake kira da “KAKA”

Uba: Shine asalin sunan Mahaifi a gida. Kuma wasu lokutan ana kiranshi da “baba”. Hakazalika akanyi anfani da sunan ga ƴan uwan mahaifi , Wa ko Ƙanin mahaifi.

Uwa: shine asalin sunan Mahaifiya wacce ta haifi ƴaƴa a gida. Kuma akan kira ta da “MAMA”

Kawu: wannan suna ne da ake kiran Wa ko ƙanin mahaifiya da shi a hausa

Goggo: wannan shine sunan da ake kiran Ya ko ƙanwar mahaifi a ƙasar hausa

Inna: wannan shine sunan da ake kiran Ya ko ƙanwar mahaifiya a gida don gamsarwa maimakon a kirasu da asalin sunansu na yanka.

Ɗan uwa: kalma ce da ake kiran duk wani ɗa namiji da ya haɗa mahaifi ko mahaifya a gida. Hakazalika ana amfani da kalmar wajen kiran wani wanda keda dangantaka da wani iyali. A wasu lokutan akan yi amfani da kalmar wajenkiran wani wanda aka haɗa ƙauye ko gari ko addini dashi.

Ƴar uwa: kalma ce da ake kiran duk wani ɗiya mace da ta haɗa mahaifi ko mahaifiya a gida. Hakazalika ana amfani da kalmar wajen kiran wani wanda keda dangantaka da wani iyali. A wasu lokutan akan yi amfani da kalmar wajenkiran wani wanda aka haɗa ƙauye ko gari ko addini dashi.

Wa: Kalma ce da ake nuni ga namiji babba wanda ya girma wani daga iyali gida.

Ƙane: Kalma ce da ake nuni ga namiji wanda ƙarami ne ko an girmeshi a gida ko cikkin iyali.

Ƴa: Kalma ce da ake nufin yaya babba ta mace a iyali.

Ƙanwa: Kalma ce dake nufin wacce aka girma cikin iyali

ɗanɗan ƙanin ko ƙanwar mahaifiya. Watau inna ko kawu.

Jika: Suna ne da ake kiran ɗan ɗan wani, watau yaro namiji wanda ɗan ko ƴar wani ko wata ta haifa

Jikanya: Suna ne da ake kiran ɗiyan ɗan wani, watau yarinya mace wanda ɗan ko ƴar wani ko wata ta haifa

Tattaɓa Kunne: suna ne da ake kiran ɗan ɗan kakan kaka

Ɗan Uba: shine Wa ko ƙane namiji daga mahaifi ɗaya amma kowa da mahaifiyarsa.

Ƴar Uba: Ya ko ƙanwa mace daga mahaifi ɗaya amma kowa da mahaifiyarsa.

Agola: idan mace ta baro wani gida da yaro ta sake wani aure zuwa wani iyali har ta tafi da wancen ɗan zuwa gidan “ to wannan ake kira da agola”. Agola suna ne da ake kiran ɗa ko ƴa dake zaune cikin iyali amma ba maigida ya haifeshi ba. Watau mahaifiyarshi daga wani gida ta haifeshi.

Uwar Gida: wannan kalma ana amfani da ita wajen kiran mata ta farko ga mutum. Kuma akanyi amfani da ita wajen kiran matan aure.

Amarya: Laƙani ne da akewa matar da aka aura ba da dadewa ba. Sannan akan kira matar da aka aura a ƙarshe a gida.

Ango: Wannan laƙani ne da ake kiran wanda yayi sabon aure ko da kuwa ba auren fari bane.

Mowa: wannan kalma ce da ake amfani da ita wajen kiran matar da aka fi so a gida, watau matar da miji ya fi so a gida.

Bora: kalma ce da ake kiran matar da miji baya sonta sosai a gida.

Suruki: Wannan suna ne da ake kiran mahaifin miji ko mata don nuna girmamawa a maimakon ainihin sunansa.

Suruka: Mahaifiyar mata ko miji

Yaya/Yadikko/Inna: Wannan suna ne da ƴaƴa ke kiran sauran matan ubansu ko wanda ke riƙonsu a wasu lokutan

Iya: Suna ne da ƴaƴa ke laƙawa mahaifiyarsu[1].

Bibiliyo[gyara sashe | gyara masomin]

Madauci, Ibrahim. (1968). Hausa customs. Isa, Yahaya., Daura, Bello. [Zaria]: Northern Nigerian Pub. Co. ISBN 978-169-097-6. OCLC 489903061.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 Madauci, Ibrahim. (1968). Hausa customs. Isa, Yahaya., Daura, Bello. [Zaria]: Northern Nigerian Pub. Co. pp.35-38. ISBN 978-169-097-6.