Zambo
Zambo, ɗan uwan habaici ne sai dai shi zambo ya fi habaici tsanani dan haka zamu iya cewa zambo zagi ne na kaitsaye ana yinsa ne don a tozarta mutum a idan jama'a. Wajen yin sa a kan ɗauki wani hali na mutum ko sifa ko ɗabi'unsa a yi masa zambo da shi. Zambo a wani ƙaulin kalmomi ne irin na ɓatamin da ake yin amfani da su domin muzgunawa wasu ko tozartawa ta hanyar yin amfani da kwatanta kama ko hali ko ɗabi'a da wasu munanan hali ko sifa don tozarta mutum.
Asalin Zambo
[gyara sashe | gyara masomin]Asalin zambo daɗaɗɗen abu ne a cikin tarihin hausawan gargajiya kuma zambo ba ararriyar kalma ba ce domin ta samo asali ne tun a lokacin da al'umma suka kafu. Kalmar zambo bahaushiyar kalma ce ba arota aka yi ba zambo a cikin Larabci yana nuna ma'ana al amma kenan babu aro a cikin kalmar zambo
Dalilin yin zambo
[gyara sashe | gyara masomin]- Rowa
- Adawa
- Husuma
- Tsoratarwa
- Raha
- Domin hana shishshigi.[1]