Zulai Daya
Hajiya Zulai Abdullahi Daya (an haife ta ranar 1 ga watan Junairun shekarar 1945 - 6 ga Nuwamban shekarar 2019). Ta kasance tsohowar malamar makaranta wadda ta yi ayyuka a ma’aikatu da dama har ya kai ga ta shugabanci makarantun Sakandari, Firamare da kuma makarantun koyar da malamai da daman gaske, ta samu shahara bisa kasancewarta mace ta farko da ta fara yin karatun digiri a jihar Yobe.[1]
Rayuwar farko da Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Hajiya Zulai Abdullahi Daya ne a garin Daya da ke karamar hukumar Fika a jihar Yobe.
Ta fara karatun Firamare dinta ne a garin Daya (Daya Junior Primary School) daga shekara ta 1951 zuwa 1953, sannan kuma ta halarci makarantar ‘yan mata ta "Probincial Girls School" a garin Maiduguri a tsakanin shekara ta 1954 zuwa shekara ta 1959, daga nan ne kuma ta hanzarta zuwa kwalejin horar da malamai mata da ke Maiduguri a shekara ta 1961 zuwa 1963, bayan da ta kammala ne kuma sai ta sake nutsa karatunta a wannan makarantar a shekara ta 1965 zuwa 1967, sannan kuma ta sake dawowa kwalejin horar da mata da ke Maidugurin don kara samun wani horo.
Zulai Daya ta kuma halarci jami’ar Abdullahi Bayero College a wancan lokacin, wadda a yanzu kuma ake kiran makarantar da suna Bayero Unibersity Kano (BUK) daga shekara ta 1967 zuwa 1972, inda ta samu shaidar karatun digiri kan harshen Nasara (Ingilishi).
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Zulai Daya ta kasance malamar makaranta a jihar Yobe, inda ta yi aiyuka a wurare daban-daban da suka hada da koyarwa a Firamaren ‘Damboa Primary School’ daga shekara ta 1962-1964, malamar makaranta a Godowoli Primary School 1965, wata uku kacal ta yi a wannan makarantar, sai ta sake komawa zuwa sakandarin SPS da ke Potiskum a matsayin malama daga 1966 zuwa 1967.
Ayyukanta ba su tsaya haka ba, ta kuma yi aiki har ta rike shugabar makarantar Firamare ta (Kara Primary) da ke Potiskum a 1966 zuwa 1967, ta koyar a sakandarin gwamnati da ke Yerwa a garin Maiduguri a tsakanin shekara ta 1972 zuwa 1973, ta kuma koyar a GGC da ke Maiduguri a shekara ta 1973 zuwa 1978, haka zalika, ta rike mukamin mataimakiyar shugaban makarantar mata ta GGC da ke Maiduguri, da kuma mataimakiyar shugaban makarantar koyar da malamai ta mata da ke Maiduguri a 1978 zuwa 1979.
Shahararta a fannin koyarwa bai kuma tsaya haka nan ba, ta kuma sake zama shugabar sakandarin ‘yan mata GGSS da ke garin Miringa a garin Biyu a shekara ta 1979, shugaban kwalejin koyar da malamai mata WTC da ke garin Nguru a shekara ta 1979 zuwa 1980, haka ta kuma yi aiki a ma’aikatar ilimi ta garin Maiduguri a shekara ta 1980 zuwa 1984, ta sake zama shugaban makaranrar mata ta GGC Maiduguri a shekara ta 1984 zuwa 1985, shugaban makarantar gwamnatin tarayya ta mata da ke Potiskum a shekara ta 1985 zuwa 2001, ta kuma kasance daga cikin hadakar bibiyar sha’anin ilimi tun a 2001 zuwa 2005 a matsayin babbar jami’a.
Zulai ta sance a cikin kungiyoyin mata daban-daban da suke kokarin ilmantar da ‘ya’ya mata da kuma kokarin daura su a hanyar da ta dace a kowane lokaci domin su zama mata na gari a rayuwarsu ta gaba, haka kuma ta kasance daga mata masu kishin iliminsu, hakan ne ya ba ta damar nutsa dukkanin gudunmawarta a sha’anin koyarwa domin daukaka darajar ilimi.
Hajiya Zulai Abdullahi Daya, ita ce mace ta farko a garin Daya da ta fara zurfafa karatunta wacce har ta kawo ga matan da ta taka a rayuwa, wadda hakan ya kai ta zuwa cikin fitattun mata. Ta yi ritaya a aikin gwamnati ne a matsayin babbar ma’aikaciya, inda kuma ta samu sarautar Magaram na Daya.
Rasuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Zulai ta rasu ranar 6 ga watan Nuwamban shekarar 2019 tana da ‘ya’ya biyar da kuma mijinta.[2]