Ƙaho

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Kaho/Hijama wata hanya ce da ake neman lafiya daga cututtuka da suka damu Dan adam. Kaho ya samo asali tun iyaye da kakanni kuma anayin shi musamman a kasar Hausa.

Yadda Ake Kaho[gyara sashe | gyara masomin]

Shi dai kaho ana yinsane a gargajiyancde ta hanyar amafani da kahon dabba wanda ka sarrafa, musamman ma kahon kananan dabbobi kamar raguna, awaki da Tamaru. Akan yanka kahon a gogeshi dai-dai yadda zai bada damar kafashi a cikin mutum. Idan za'ayiwa mutum Kaho, wanzami zai dasa kahon a dai dai inda ke da tararren mataccen jini a jikin mutum. A na amfani da aska domin yin tsaga a dai dai wajen kafun a sanya kahon a rufe, sai kuma a sanya baki a saman kahon wanda yakeda dan rami karami, sai wanzami yasa bakinsa akan ramin yayita hurawa yana zuqowa har sai mataccen jinin ya fito duka. A yau, cigaban zamani ya zamanantar da yadda ake kaho sannan an samarda kayan aiki na roba ba tareda anyi amfani da kaho ba, [1]

Amfanin Ƙaho ga Ɗan Adam[gyara sashe | gyara masomin]

Asali[gyara sashe | gyara masomin]

Kaho ya samo asali ne tun shekaru dubbai da suka gabata a kasar Sin, inda suke amfani da shi wajen maganin matsalolin jini da ciwon jiki. Ka ga ke nan ba aikin likitancin zamani irin namu ba ne.[2][3][4]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]