Jump to content

Ƙauri

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
kauyen kauri

Ƙauri dai al'ada ce da hausawa ke yin ta ga mai jego wato macen da ta haihu.

Tarihi ya nuna tun ƙarni na baya al'adar hausa ta samo asali wanda yanzun ba za'a iya cewa ga iya adadin lokacin data samo asali ba, to amman ita wannan al'adar hausawa kanyi ta ne domin farin cikin samun ƙaruwa ta haihuwa.

Yaushe ake ƙauri

[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan maijego ta haihu da ƙwana uku (3) to akan kawo ma maijego naman kai na shanu, ko a yanka ɗan akuya, ko kuma a dafa ganda ana rabawa maƙota ko mutanen da suke zuwa barka. Ƙauri dai shi ne dan ƙaramin biki dake fara wakana kanin zuwan bikin suna idan maijego ta sami ƙaruwa ta haihuwa. [1]