100 Bucks
100 Bucks | |
---|---|
Asali | |
Ƙasar asali | Namibiya |
Characteristics | |
External links | |
Specialized websites
|
100 Bucks gajeren fim ne na Namibia na shekarar 2012 wanda Oshosheni Hiveluah ya ba da umarni kuma Cecil Moller da Mutaleni Nadimi suka shirya. Fim din ya mayar da hankali ne kan labarin tafiyar dalar Namibiya 100-note, da ta tashi daga hannun masu dukiya zuwa hannun masu buƙata da ta hannun barayi.[1][2]
Fim din ya samu kyakykyawan sharhi kuma ya samu kyaututtuka da dama a bukukuwan fina-finai na duniya. Fim ɗin ya lashe lambar yabo ta masu sauraro a 2012 Namibia FFilm and Theater Awards. A shekarar 2011, Oshosheni ya sami lambar yabo ta Features Africa First Prize don 100 Bucks. 100 Bucks kuma ya sami lambar yabo ta 2012 Namibia Theatre and Film Choice Choice. 100 Bucks an haska shirin a Landan ta ƙungiyar masu zaman kansu ta AfricAvenir Windhoek da kuma a birnin New York a shekarar 2012 a Bikin Fina-Finai na Ƙasashen Afirka (ADIFF).[3]
Yan wasan shirin
[gyara sashe | gyara masomin]- Steven Afrikaner a matsayin Tsotsi 2
- Sylvanie Beukes a matsayin Dantagob
- Girley Jazama a matsayin Maria
- Perivi Katjavivi a matsayin Nolan
- Victor Mtambanengwe a matsayin Elvis
- David Ndjavera a matsayin Taxi Driver
- Lynn Strydom a matsayin Tameka
- Tanya Terblanche a matsayin Reyna
- Ripuree Tjitendero a matsayin Lia
- Onesmus Uupindi a matsayin Tsotsi 1
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "10 African films to watch out for, N°12". africultures. Archived from the original on 31 March 2021. Retrieved 10 October 2020.
- ↑ Nelmes, Jill; Selbo, Jule (2015-09-29). Women Screenwriters: An International Guide (in Turanci). Springer. ISBN 978-1-137-31237-2. Archived from the original on 2020-10-20. Retrieved 2020-10-11.
- ↑ "ADIFF 2012 - 'Spotlight On Namibia' Features A Great-Looking Lineup Of Short Films You Should See". shadowandact.com (in Turanci). Archived from the original on 2020-07-01. Retrieved 2020-07-01.