APACHE

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Suna = Apache HTTP Server
Tambari = Apache Software Foundation Logo (2016).svg
Mai wallafawa = Robert McCool
Makeri = Apache Software Foundation
Manhaja = Cross-platform
Harshe = English
Iri = Web server
lasisi = Apache License 2.0
https://httpd.apache.org/

Manhajar APACHE kuma ana amfani ne da ita wajen aiwatar da sadarwa a ka’idar mu’amala da fasahar Intanet. Manhaja ce mai dauke da titi, ko hanya, da kuma ka’idar da ke sawwake wa titin isar da sako daga kwamfuta zuwa kwamfuta. A takaice dai, masarrafar ka’idar sadarwar Intanet ce (Web Serber), kuma kyauta ake samunta, kamar yadda ake samun wasu daga cikin nau’ukan babbar manhajar LINUd kyauta. Kamfani ko hukumar Facebook sun zabi yin amfani da manhajar APACHE ne don ita ce ta fi dacewa da babbar manhajar LINUd wajen adanawa da kuma sarrafa bayanai. A takaice dai, ita ce manhajar da ta fi alakantuwa da babbar manhajar LINUd wajen samun ka’idar sadarwa ta Intanet, kamar yadda babbar manhajar Windows ta fi dangantuwa ga ka’idar sadarwar Intanet mai suna Internet Information System, wato: IIS na kamfanin Microsoft kuma wanda ke dauke da’iman cikin babbar manhajar Windows.