Abdoulaye Harouna
|
| |||||||||||||||||||||||
| Rayuwa | |||||||||||||||||||||||
| Haihuwa | Niamey, 12 Disamba 1992 (33 shekaru) | ||||||||||||||||||||||
| ƙasa | Nijar | ||||||||||||||||||||||
| Karatu | |||||||||||||||||||||||
| Makaranta |
Miami University (en) | ||||||||||||||||||||||
| Sana'a | |||||||||||||||||||||||
| Sana'a |
basketball player (en) | ||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||
Abdoulaye Harouna Amadou (an haife shi a 12 ga Disamban shekarar 1992) shi ɗan wasan ƙwallon kwando ne daga ƙasar Nijar wanda ke buga ƙwallon kwando ta FAP da kuma Niger . Ya buga wasan ƙwallon kwando na Miami RedHawks.[1]
Rayuwar farko
[gyara sashe | gyara masomin]Harouna wanda aka haife shi kuma ya girma a Niamey, Nijar, daga baya ya koma Amurka don buga wasan ƙwallon kwando na Kent ta Kudu.[2]
Kwarewar sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Harouna ya fara aikin sa ne tare da AS Nigelec a cikin kasar sa ta Nijar. A watan Oktoban shekarar 2019, Harouna yayi wasa a cikin Wasannin BAL na cancantar shekarata 2020 tare da ƙungiyar.
A watan Mayun shekarar 2021, ya koma ƙungiyar ƙwallon kwando ta Kamaru ta FAP Kwando don buga wasan farko na BAL . Harouna ya jagoranci FAP wajen zira kwallaye da maki 19.3 a kowane wasa kuma ya jagoranci tawagarsa zuwa wasan kusa dana karshe.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Abdoulaye Harouna - Men's Basketball". Miami University RedHawks (in Turanci). Retrieved 12 May 2021.
- ↑ "Abdoulaye Harouna - Men's Basketball". College of Southern Idaho Athletics (in Turanci). Retrieved 24 May 2021.