Jump to content

Aburi Botanical Gardens

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Aburi Botanical Gardens

Bayanai
Iri botanical garden (en) Fassara
Ƙasa Ghana
Tarihi
Ƙirƙira 1890
Aburi Botanical Gardens da Itatuwan Dabino a cikin Aburi

Aburi Botanical Gardens wani lambun tsirrai ne a Aburi da ke yankin Gabashin Kudancin ƙasar Ghana.

Lambun ya mamaye yanki mai girman hekta 64.8. An buɗe shi a watan Maris, shekarar 1890 kuma Gwamna William Brandford-Griffith da Dr John Farrell Easmon, likitan Saliyo ne suka kafa shi.[1] Kafin a kafa lambun, wurin ne da aka gina gidan tsafi a cikin shekarar 1875 don jami'an gwamnatin Gold Coast. A lokacin gwamnan William Brandford-Griffith, wani ɗan mishan na Basel kuma ɗan Moravian na Jamaica, Alexander Worthy Clerk, ya kula da aikin share fili a kewayen gidan tsafi don fara Sashen Botanic.[2] A cikin 1890 William Crowther, dalibi daga Royal Botanic Gardens, Kew, an nada shi mai kula da lambun na farko.[3] Lambunan sun taka muhimmiyar rawa wajen karfafa noman koko a cikin Kudancin Ghana, ta hanyar samar da koko mai arha da bayanai game da hanyoyin noman kimiyya.[4] Bayan an aika Hevea brasiliensis zuwa Aburi daga Kew a cikin shekarar 1893, lambunan sun kuma karfafa samar da roba a Ghana.[5]

  1. Richard Kwame Debrah, The Beautiful Aburi Botanic Garden of Ghana, GhanaWeb, 4 June 2005
  2. "Fiarfield House [sic, Jamaica-Aburi (Fairfield House) - BM Archives". www.bmarchives.org. Retrieved 2019-10-05.
  3. Aburi Botanic Gardens. Botanic Gardens Conservation International
  4. Kwamina B. Dickson, A Historical Geography of Ghana, 1969, Cambridge University Press, p. 166. J. H. Frimpong-Ansah, The Vampire State in Africa: The Political Economy of Decline in Ghana, 1992, Africa World Press, p. 123.
  5. Kees Burger, Hidde P. Smit, The Natural Rubber Market: Review, Analysis, Policies and Outlook, 1997, Woodhead Publishing, p. 213.