Affiong Williams
Affiong Williams | |
---|---|
Williams in 2014 | |
Haihuwa | 1987 |
Dan kasan | Nigerian |
Affiong Williams listen ⓘ dan kasuwan Najeriya ne daga jihar Cross River. Ita ce ta kafa kuma Shugabar kamfanin Reel Fruit, wani kamfani a Najeriya da ke sarrafa da rarraba kayan marmari da ake nomawa a cikin gida. Ta auri Tayo Oviosu, Shugaba na kamfanin kudi Paga.[1]
Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Williams ta kammala karatun digiri ne a fannin ilimin halittar jiki da tunani daga Jami'ar Witwatersrand, Afirka ta Kudu . Ta kuma yi difloma ta biyu a fannin kasuwanci a jami'ar. Ta kuma halarci Makarantar Kasuwanci ta Stanford inda ta shiga cikin Shirin Canjin iri na 2018.
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Bayan kammala karatun digiri, ta yi aiki tare da Endeavor Afirka ta Kudu daga 2008 zuwa 2012 inda ta kai matsayin Manajan Fayil. Ta dawo Najeriya a 2012 kuma ta fara aikin ReelFruit, sana'arta. An ce ta fara kamfanin ne a gidanta da ke Surulere, tare da ajiyar farko na $8,000.[2] [3][4] [5]
Rayuwa ta sirri
[gyara sashe | gyara masomin]Ta auri Tayo Oviosu, wanda ya kafa kuma Shugaba na kamfanin kudi Paga. [6]
Kyaututtuka da karramawa
[gyara sashe | gyara masomin]Ita dai Forbes ta sanya ta a cikin ƴan kasuwan da suka fi ƙwarin gwiwa a Afirka a 2015. ReelFruit ta lashe Gasar Kasuwanci ta Mata ta Duniya a Netherlands.[7][8][9]
In March 2023, Affiong Williams was named among the "15 African Female Founders You Should Know In 2023" by African Folder.[10]
Magana
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Tayo Oviosu and Affiong Williams are relationship goals". Techpoint Africa (in Turanci). April 14, 2017.
- ↑ "Affiong Williams | Africa 2017 | Global Business Forum". globalbusinessforum.com (in Turanci). Archived from the original on 2018-07-17. Retrieved 2018-07-17.
- ↑ Essiet, Daniel. "Her road to success". The Nation. Retrieved 16 July 2018.
- ↑ Ijewere, Esther. "#PROFILE| MEET AFFIONG WILLIAMS, THE YOUNG LADY INTRODUCING A NEW SNACK INTO THE NIGERIAN MARKET". Women of Rubies (in Turanci). Retrieved 2018-07-17.
- ↑ Adekoya, Femi (17 March 2017). "Affiong Williams: Low consumer purchasing power affecting businesses". The Guardian (Nigeria). Archived from the original on 17 July 2018. Retrieved 16 July 2018.
- ↑ Paga
- ↑ Dolan, Kerry A. (13 June 2015). "Africa's Most Promising Young Entrepreneurs: Forbes Africa's 30 Under 30 For 2015". Forbes. Retrieved 15 July 2018.
- ↑ Onehi, Victoria (14 July 2016). "Affiong Williams Makes Forbes Africa's Billionaire List". Daily Trust. Archived from the original on 17 July 2018. Retrieved 16 July 2018.
- ↑ Essiet, Daniel. "Her road to success". The Nation. Retrieved 16 July 2018.
- ↑ "15 African Female Founders You Should Know In 2023". African Folder. Retrieved 12 March 2023.