Jump to content

Ahmad Garba Gunna

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ahmad Garba Gunna
Rayuwa
Haihuwa 1 ga Janairu, 1975 (49 shekaru)
Sana'a

Malam Ahmad Garba Gunna, (an haife shi ranar 1 ga watan Janairu, 1975), a garin Yakila a Gunna, yana da matsayi na musamman na zama jikan Malam Attahiru I, Sarkin Gunna na 5, wanda ya yi sarauta daga shekara ta 1928 zuwa 1954. Shi ne sabon Sarkin Kagara, kafin ya zama sabon zaɓaɓɓen Sarkin Kagara, ana shine Dagacin Gunna da kuma Dan Majen Kagara.[1] Bayan rasuwar Sarkin Kagara Alhaji Salihu Tanko a ranar 2 ga watan Maris, shekarar 2021, Majalisar Sarakunan Masarautar ta zaɓe shi. Kusan sarakuna 8 ne suka tsaya takarar kujerar sarautar, amma ya doke sauran ƴan takara a zaɓen da sarakunan masarautar Kagara 14 suka gudanar.

Garba Gunna ya fara karatun firamare a makarantar firamare dake Gandun Albasa. Daga nan ya wuce Government Day Secondary School Sharada, duk a cikin Kano. Bayan ya kammala karatunsa na Sakandare, ya shiga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kebbi, inda ya karanta Mulki da tsare-tsare. Sannan kuma ya samu digirin Bsc a fannin lissafi a Jami’ar Tarayya Abuja. Bayan kammala karatunsa ya yi bautar ƙasa a jihar Kwara.

Ya yi aiki da hukumar tara haraji ta jihar Neja, inda ya riƙe muƙaddashin shugaban hukumar.

Alhaji Ahmad Garba yana da aure da ƴaƴa huɗu.

  1. Yusuf, Ahmad (7 April 2021). "Gwamna Abubakar Bello na jihar Neja ya zabi Ahmed Garba matsayin Sabon sarkin Kagara". hausa.legit.ng. Retrieved 22 October 2023.