Masarautar Kagara
Masarautar Kagara | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | administrative territorial entity (en) da Emirate (en) |
Ƙasa | Najeriya |
Masauratar Kagara masarauta ce dake a jihar Neja wadda take a Ƙaramar Hukumar Rafi a cikin garin kagara, Masarautar tana ƙarƙashin Gundumar Sanatan Neja ta gabas kuma kagara itace babban birnin ƙaramar hukumar rafi.[1] sabon sarkin da aka naɗa a masarautar kagara bayan rasuwar tsohon sarki Alhaji Salihu Tanko shine, Alhaji Ahmad Garba Gunna[2][3][4] kafin a naɗa sabon sarkin na uku shine ɗan majen Kagara kuma mataimakin mai tara haraji na jihar Neja. A garin Kagara aka haifa shahararren marubucin littafin nan mai suna magana jarice Alhaji Abubakar Imam ya rubuta littafin Hausa da dama. Masarautar itace babbar masarauta a ƙaramar hukumar Rafi masarautu irin na Pandogari sune ke biye da ita a girma.[5]
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Alhaji Ahmed Garba shine Sarkin kagara na uku bayan rasuwar sarki na biyu Alhaji Salihu Tanko mai kagara.
Sarauta
[gyara sashe | gyara masomin]Masu mulki
[gyara sashe | gyara masomin]No. | Suna | Fara Mulki | Karshen Mulki |
---|---|---|---|
1 | Ahmadu Attahiru | ||
2 | Alhaji Salihu Tanko | ? | 2 ga Maris 2021 |
3 | Alhaji Ahmad Garba Gunna | 7 ga Aprilu 2021 | zuwa yanzu |
Dam ɗin Kagara
[gyara sashe | gyara masomin]Garin yana da masana'antar sarrafa talc. An fara gina madatsar ruwa a shekarar 1979 akan kuɗi naira biliyan biyar. Jami'ar Fasaha ta Tarayya Minna ta gudanar da kimanta tasirin Muhalli ga Babban Kogin Neja da Hukumar Raya Karkara (UNRBDA). Kimanin Naira biliyan uku aka biya a watan Fabrairun shekara ta 2002, lokacin da Ministan Albarkatun Ruwa, Muktar Shagari, ya bai wa ɗan kwangilar wa'adin kammala madatsar ruwan zuwa watan Disamba na wannan shekarar. A watan Fabrairun shekara ta 2004 Ƙaramin Ministan Albarkatun Ruwa, Mista Bashr Ishola Awotorebo ya ziyarci wurin madatsar ruwan, a sakamakon haka ya kira ɗan kwangilar da ya yi bayanin jinkirin aikin. A watan Agustan 2004, yayin da yake gabatar da famfunan hannu guda 500 daga Gwamnatin Tarayya ga Gwamnan Jihar Neja, Abdul-ƙadir Kure, Mukhtar Shagari ya ce aikin dam ɗin zai iya lalacewa saboda rashin amincewa da kasafin kuɗin. A watan Agusta na 2007, Bala Kuta na Jam'iyyar ANPP wakilin Majalisar Dokoki ta Najeriya, ya yi alƙawarin taimakawa da aikin madatsar ruwan.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Ahmadu Mai Shanu, Abubakar (2 October 2021). "Bandits kill two soldiers, injure 12 others in attack on Niger community – Governor". premium times. Retrieved 10 October 2021.
- ↑ Nasiru Batsari, Mustapha (7 April 2021). "An Nada Sabon Sarkin Kagara A Jihar Nema Najeriya". VOA Hausa.Com. Retrieved 11 October 2021.
- ↑ Ahmad Maishanu, Abubakar (7 April 2021). "Kagara gets new emir". Premium times. Retrieved 16 October 2021.
- ↑ "Ahmed Garba Gunna Ya Zama Sabon Sarkin Kagara Na Uku". www.hausa.leadership.ng. 8 April 2021. Archived from the original on 16 October 2021. Retrieved 16 October 2021.
- ↑ Salisu, Ahmed (1 September 2019). "Tarihin Alhaji Abubakar Imam". dw.hausa.com. Retrieved 18 December 2021.