Abubakar Imam

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Alhaji Abubakar Imam, shahararren marbucin Hausa. Wanda ya wallafa littatafai da dama, cikinsu akwai Magana Jari Ce, Ruwan Bagaja da sauransu. Marabucin ya samu shahara a Duniyar Nazarin Harshen Hausa. Ya zamo edita na farko na jaridar Arewa, Gaskiya Ta Fi Kwabo.

Yanzu haka a na nazarin talife-talifen da ya yi a manya da kananan makarantu a Nijeriya.

Tarihin Rayuwarsa[gyara sashe | Gyara masomin]

An haifi Alhaji Dr. Abubakar Imam, O.B.E; C.O.N.; LL.D (Hon.) N.N.M.C. a Cikin shekarar 1911 a cikin garin Kagara sa'an nan tana cikin lardin Kwantagora, yanzu kuwa Jihar Neja. [1]Ya yi makaranta a Katsina Training College kuma ya kama aikin malanta a Makarantar Midil ta Katsina a shekarar 1932. Yana da shekara 22 ya rubuta 'Ruwan Bagaja'. Ganin kwazonsa wajen kaga labari mai ma'ana ya sa Dr. R.M. East, shugaban Ofishin Talifi na Zariya, ya roki a bada shi aro daga Katsina ya yi aikin rubuce-rubuce a Zariya. A zaman sa na Zariya ne Abubakar Imam ya wallafa littafin Magana Jari Ce 1-3, Ikon Allah 1-5 da Tafiya Mabudin Ilimi.[2] Abubakar Imam shi ne editan jaridar Gaskiya Ta fi Kwabo na farko kuma shi ne ma ya rada mata sunan ta.

Tasirin Talifinsa Ga Harshen Hausa[gyara sashe | Gyara masomin]

Masana/Manazarta Harshen Hausa sun tabbatar da cewar har ya zuwa yanzu babu wani marubuci da ya baiwa Adabin Hausa gudunmowa ta musamman fiye da Alhaji Abubakar Imam, domin kasancewarsa marubuci mai cikakkiyar basira da fasahar shirya labarai iri daban-daban.

Duba da muhimmancinsa ne ma, ya sa masana su ka sanya talifinsa cikin jadawalin darussan Hausa a Makarantun Sakandire da kuma Jami'o'i.

Tunawa Da Shi[gyara sashe | Gyara masomin]

Duba ga irin gudunmowa da ya bayar ga Talifi da Aikin Jarida, Masarautar Burtaniya ta girmama Alhaji Abubakar Imam da lambar girma ta O.B.E, Order of British Empire. Daga bisani kuma gwamnatin Nijeriya ta girmama shi ta tata lambar makamanciyar O.B.E, wato C.O.N.

Yanzu haka gwamnatin Jihar KanoTa sanya sunan shi a Babban Asibitin Kula da ma su Yoyon Fitsari, wato Abubakar Imam Urology Hospital, da ke Birnin Kano.

Inda Aka Duba[gyara sashe | Gyara masomin]

Shafin Waje[gyara sashe | Gyara masomin]

Yabon fiyayyen halitta kammalalle

Wadansu littatafan da Alhaji Abubakar Imam ya rubuta sun hada da Tarihin Annabi (S.A.W) Kammalalle da kuma Karamin Sani Kukumi.Hakika,Alhaji Abubakar Imam yana sahun gaba a manyan taurarin adabin Hausa Kuma wanda Har ila yau bashida tamka A Fannin Kaga Labarai.

  1. Abba Musa (2009-02-15). "ABB MUSA: Gundarin Tarihin Alhaji Dr. Abubakar Imam Kagara". abbamusa.wordpress.com. Retrieved 24 June 2010. 
  2. Bashir Ahmad (2011-07-13). "DANDALIN BASHIR AHMAD: Takaitaccen Tarihin Dr. Abubakar Imam". Dandalinbashir.blogspot.com. Retrieved 2013-11-08.