Ɗan jarida

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
ɗan jarida
Training to be journalists (10730417125).jpg
sana'a
subclass ofmedia professional, author, sana'a Gyara
field of this occupationjournalism Gyara
ISCO-88 occupation code2451, 2642 Gyara
category for eponymous categoriesCategory:Wikipedia categories named after journalists Gyara
Rediyo
Talabijin
Dan jarida

Ɗan jarida shine mai samo labarai yana yadawa a gidajen talabijin da jaridu. Ana samun Dan jarida mai zaman kansa ko kuma wanda zai rinka yima wata kafar yada labarai, Rediyo ko Talabijin. Akwai ire iren Yan jaridu kamar, Mai rahoto (wanda yake bincike kuma ya rubuta sannan ya kawo rahoto.) Yan jaridu suna rubuta labarai da sharhi ga kafafen yada labaru. Suna yin bincike ne da hira da mutane da tambayoyi wajen rubuta labaru da rahotannin su. Dolene masu rubuta labarai da sharhi su zama masu fadin gaskiya. Fadin gaskiya yana da matukar muhimmancin gaske ga aikin jarida. Idan Dan jarida ya zama baya fadin gaskiya a labaru ko rahotannin sa to yakan fuskanci hukunci na dakatarwa ko ma kora bakidaya.

Hadari ga Dan Jarida[gyara sashe | Gyara masomin]

masu dauko rahoto na fuskantar matsaloli wajen dauko rahoton

Sau tari Yan Jarida kan samu kawunan su a hadurra, musamman ma wajen da ake samun rikicin ta'addanci ko fagen yaki. Hakanan daga cikin hadari na aikin jarida akwai rashin samun yanci yin aikin rahoto a wasu kasashe. Wani Kwamiti mai kare Yan Jarida yayi rahoton cewa daga 1 ba Disamba na 2010, akwai yanjaridu 145 dake a daure a jarum a fadin duniya. Kasashe goma wadanda akafi samun Yan jarida a gidan kurkuku sune Turkiyya (95),[1] Sin (34), Iran (34), Eritrea (17), Burma (13), Uzbekistan (6), Vietnam (5), Cuba (4), Ethiopia (4), da Sudan (3.[2]

Rabe raben aikin jarida[gyara sashe | Gyara masomin]

mai daukar hoto

Akwai rabe rabe masu yawa a aikin jarida.

  • Akwai mai rubutu da nazarin labarai.
  • Akwai mai rahoto na nesa, wanda ke dauko rahoto ga rediyo ko talabijin daga wani gari mai nisa koma daga wata kasar ta waje.
  • Akwai kuma Dan jarida mai duba gyare gyare da yadda labari yake.
  • Akwai kuma wanda shi aikinsa duba kuskuren rubutu.
  • Akwai kuma wanda ke gabatar da labarai.
  • Akwai mai daukar hoto.
  • Mai daukar photo da kawo rahoto
  • Mai daukar sauti

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. "Number of Jailed Journalists Nearly Doubles in Turkey". Los Angeles Times. 5 April 2012. Retrieved 6 April 2012. 
  2. Iran, China drive prison tally to 14-year high. "Iran, China drive prison tally to 14-year high (December 8, 2010). Committee to Protect Journalists. Retrieved November 18, 2011". Cpj.org. Retrieved 2013-04-16.