Jump to content

Gaskiya Ta Fi Kwabo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Gaskiya Ta Fi Kwabo
Bayanai
Iri takardar jarida
Harshen amfani Hausa
Tarihi
Ƙirƙira ga Janairu, 1939

Gaskiya Ta Fi Kwabo "gaskiya da daraja fiye da kwabo". Kwabo shi ne "kashi ɗaya bisa dari" na kuɗin Najeriya. Gaskiya ta fi Kwabo gidan jarida ne a Najeriya, wanda ake bugawa sau uku a mako. Ita ce takarda ta farko da aka fara amfani da ita a harshen Hausa, kuma tana ɗaya daga cikin littattafan farko da ke arewacin Najeriya. Editan Gaskiya Ta Fi Kwabo shi ne Abubakar Imam. A cikin shekara ta alif ɗari tara da arba'in da ɗaya 1941, an ƙara wasu shafuka a cikin Ajami zuwa jaridar ga waɗanda ba sa iya karanta rubutun Hausar boko. An ƙira su da "'Yar Gaskiya".[1]

  1. Adamu, Yusuf M. "Print and Broadcast Media in Northern Nigeria" (pdf). kanoonline.com. Kano Online. Retrieved 2007-08-01.