Pandogari garine ko kuma ƙauye ne dake a ƙaramar hukumar Rafi, Kagara ajihar Neja, Najeriya. Kagara itace shelkwatar karamar hukumar Rafi. Tsakanin pandogari da babban birnin jihar Neja wato Minna kusan 156.7km ne garin Pandogari yana akan hanyar Birnin Gwari, wadda ta zarce har Kaduna haka kuma garin Pandogari yana akan hanyar Lagos.
Pandogari tana karkashin masarautar Hakimin kwangwama wadda take a cikin garin har iyau ita Kuma masarautar pandogari tana karkashin masarautar Kagara Alhaji Idris Aliyu shine Hakimin Pandogari, shine sarki na 3 da suka mulki garin Pandogari kuma shine na 2 kasancewar ya sauka ya kuma sake zamowa hakimin Pandogari. Pandogari tanada yaruka 3 wadanda kusan sune daga kaje zaka ci karo dasu; akwai Hausawa, sai Fulani da kuma Ɓurawa duk da cewa wasu na ganin asalin garin Pandogari ɓurawa ne suka kafa shi sai dai kuma yanzu zallar su suna a kauyukan Pandogari ne suma Fulani suna a kauyukan garin a cikin kwaryar garin hausawa ne zalla sai dan sauran kabilun da ba'a rasa ba irin Yarbawa, Igbo, Kamukawa, Pongu da dai sauransu. A shekarar 2016 an samu wani rikicin Addini wanda ya haddasa rasa rayukan mutane kusan 4 ciki hada wani matashi dan Makaranta a cikin garin Pandogari, Kusan ana cewa wannan matashin shine wanda ya sabbaba rikicin tunda shine ya yada kalaman batanci ga Manzon Tsira da Rahama (S A W) a kafar sada zumunta ta Facebook, shi kuma matashin Kirista ne shiyasa rikicin yake tsakanin Musulmai da kiristoci rikicin yasa anyi kone-konen shaguna da wuraren bauta. A karshe gwamnatin jihar Neja a karkashin Abubakar Sani Bello ta aiko da jami'an tsaro aka kwantar da tarzoma.[1][2][3][4]