Jump to content

Yaren Pongu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Yaren Pongu
Yaren Pongu
Lamban rijistar harshe
ISO 639-3 png
Glottolog pong1250[1]
Yaren Pongu

Pongu (Pangu), ko Rin, yare ne na Kainji da ake magana dashi a Nijeriya . Akwai masu magana kusan 20,000. Babban cibiyarsu tana cikin garin Pangu Gari na jihar Neja, kimanin kilomita 20 kudu maso gabashin Tegina, Mariga. Yaren Pongu sunada kusanci da Yaren Ura /Ɓurawa suna jin wasu kalmomi daga cikin yaren Ura haka suma Ura suna jin wani sashe na yaren Fongu

Akwai dangin Rin 8. Suna magana da ɗan bambanci kaɗan amma yarukan suna fahimtar juna.

  • chasu
  • cha'undu
  • A'sebi
  • chagere/chamajere
  • A-baba=ubawsbaws
  • Awusi=Akwa
  • Ãzhiga
  • Awaga=awægæ

Awәgә na iya kasancewa wata ƙabila daban wacce aka haɗa ta cikin ƙungiyar Rin. Awәgә yare ne daban na Rin, kuma ana amfani dashi a wasu ƙauyuka a gabashin Zungeru. Koyaya, a yau ya kusan karewa. Blench (2012) ya sami damar yin rikodin wani ɗan magana-magana a ƙauyen Dikko, kusa da garin Luwa, Rafi LGA. An ruwaito masu magana da kyau biyu a Gidan Gambo, kusa da Pongu Gari.

  • Dettweiler, Stephen da Sonia Dettweiler (2002) 'Binciken zamantakewar jama'a na mutanen Pongu', duba nan 2002-040
  1. Hammarström, Harald; Forkel, Robert; Haspelmath, Martin, eds. (2017). "Yaren Pongu". Glottolog 3.0. Jena, Germany: Max Planck Institute for the Science of Human History.

Kara karantawa

[gyara sashe | gyara masomin]