Jump to content

Abubakar Sani Bello

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abubakar Sani Bello
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

13 ga Yuni, 2023 -
District: Gundumar Sanatan Neja ta Arewa
Gwamnan jahar Niger

29 Mayu 2015 - 29 Mayu 2023
Mu’azu Babangida Aliyu
Rayuwa
Cikakken suna Abubakar Sani Bello
Haihuwa Jihar Neja, 17 Disamba 1967 (56 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Maiduguri
Matakin karatu BSc Economics and Politics (en) Fassara
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Ma'aikacin banki
Imani
Jam'iyar siyasa Action Congress of Nigeria (en) Fassara

Abubakar Sani Bello An haife shine a ranar 17 ga watan Disamban shekara ta alif dari tara da sittin da bakwai 1967) Miladiyya.a jihar Neja, Najeriya. Ɗan siyasar Najeriya, wanda shine tsohon Gwamnan Jihar Niger, Nigeria daga ranar 29 ga watan Mayu shekarar 2015 zuwa ranar 29 ga watan Mayu shekarar 2023.[1] yanzu kuma sanata mai wakiltar Gundumar Sanatan Neja ta Arewa,a Majalisar dattawan Najeriya.

Tasowarsa da karatunsa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Abubakar Sani Bello a ranar 17 ga watan Disamba shekarar 1967.[2] Ɗan tsohon gwamnan mulkin soja na tsohuwar jihar Kano, Kanar Sani Bello. Ya yi makarantar firamare ta St. Loius da ke Kano daga 1974 zuwa 1979 sannan ya tafi Makarantar Soja ta Najeriya daga 1980 zuwa 1985, Ya yi karatu a Jami'ar Maiduguri daga 1986 zuwa 1991, inda ya sami digiri na biyu a fannin tattalin arziki. Ya yi aiki a wurare daban-daban a ƙasar nan, tun daga lokacin da ya yi NYSC, inda aka tura shi aiki a Fatakwal a sashen kasuwanci na NICOTES Services a matsayin Supervisor.[3]

Aikin siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Neman gwamna:

Alhaji Abubakar Sani Bello ya lashe zaben fidda gwani na gwamnan jihar Neja, APC a zaben 2015. Ya samu kuri’u 3,829 inda ya doke Sanata Musa Ibrahim a zaben fidda gwani. Daga baya ya ci gaba da lashe babban zaben da jimillar kuri’u 593,709. Hukumar INEC ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben a ranar 13 ga Afrilu, 2015. A ranar 9 ga Maris, 2019, aka sake zaben shi a matsayin Gwamnan Jihar Neja.[4][5]

A ranar 24 ga watan Agusta 2020, ya amince da kwamitin sulhu da sauran kwamitoci a wani taron kwamitin zartarwa na Jiha, tare da ‘yan majalisar dokoki ta kasa daga jihar karkashin jagorancin Sanata Aliyu Sabi Abdullahi da sauran shugabannin jam’iyyar. Manufar wannan kwamiti ita ce sake ginawa da kuma sake fasalin jam’iyyar domin samun kyakkyawan aiki a zabukan 2023.[6][7]

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.


Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2018-06-14. Retrieved 2018-12-19.
  2. "Abubakar Sani-Bello Archives". Vanguard News (in Turanci). Retrieved 2023-06-17.
  3. "Abubakar Sani Bello". Politicians Data (in Turanci). 2018-05-22. Retrieved 2023-06-17.
  4. https://www.premiumtimesng.com/regional/north-central/319328-gov-bello-of-niger-secures-second-term-wins-in-all-25-lgs.html
  5. https://dailytrust.com/gov-bello-defeats-nasko-with-228347-votes-in-niger
  6. https://www.thisdaylive.com/index.php/2020/08/02/x-raying-five-years-of-sani-bellos-niger/
  7. https://dailypost.ng/2020/05/25/ipac-rates-niger-state-gov-abubakar-sani-high-on-rule-of-law/