Jump to content

Aliyu Sabi Abdullahi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Aliyu Sabi Abdullahi
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

11 ga Yuni, 2019 -
District: Gundumar Sanatan Neja ta Arewa
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

6 ga Yuni, 2015 -
District: Gundumar Sanatan Neja ta Arewa
Rayuwa
Cikakken suna Aliyu Sabi Abdullahi
Haihuwa Jihar Neja, 10 ga Janairu, 1967 (57 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Mamba majalisar na 9
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party
All Progressives Congress

Aliyu Sabi Abdullahi CON (an haife shi a ranar 10 ga watan Janairun shekara ta 1967) ɗan siyasar Najeriya ne, kuma Sanata mai wakiltar Neja ta Arewa a Majalisar Dattawan Jihar Neja a Majalissar Dokoki[1] ta Majalisya ta 8 da Majalisar Dokoki ta 9.[2][3][4] Shi ne mataimakin shugaban bulala a majalisar dokokin Najeriya ta tara.[5][6]

Sana'ar siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Abdullahi ya halarci zaɓen Sanatan Neja ta Arewa a ranar 28 ga Maris, 2015 kuma aka bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen.[7][8] A watan Fabrairun shekara ta 2019 a zaɓen Sanatan Neja ta Arewa, an sake zaɓensa a matsayin Sanata bayan da ya samu ƙuri’u 161,420, yayin da Honarabul Muhammad Sani Duba na PDP ya samu ƙuri’u 77,109.[9]

A watan Oktoban 2022, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ba shi lambar yabo ta ƙasa ta Najeriya kwamandan The Order Of Niger (CON).[10]