Jump to content

Aba

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Aba


Wuri
Map
 5°07′00″N 7°22′00″E / 5.1167°N 7.3667°E / 5.1167; 7.3667
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin NajeriyaJihar Abiya
Ƙananan hukumumin a NijeriyaAba ta Kudu
Yawan mutane
Faɗi 1,160,000 (2022)
• Yawan mutane 16,111.11 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Turanci
Labarin ƙasa
Yawan fili 72 km²
Wuri a ina ko kusa da wace teku Aba River (Nigeria)
Altitude (en) Fassara 205 m
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo 450
Kasancewa a yanki na lokaci
Tsarin lamba ta kiran tarho 082
Wasu abun

Yanar gizo abiastate.gov.ng
Aba Main Park
hotel din aba

Aba Birni ne, da ke a jihar Abia, kudu-maso-gabashin Najeriya, kuma itace cibiyar kasuwanci na jihar Abia. A yayinda aka samar da jihar Abia a shekara ta 1991, An raba Aba zuwa kananan hukumomi biyu; Aba ta kudu da kuma Aba ta yamma. Aba ta kudu itace mafi muhimmanci kuma itace cibiyar Jihar Abiya. Birnin tana nan a gabar kogin Aba. Aba tana da kauyuka kaman su Aba-Ukwu, Eziukwu-Aba, Obuda-Aba, Umuokpoji-Aba da makamantansu. Kabilar "Ngwa" na iyamuaran Najeriya suka samar da jihar Aba a matsayin kasuwa daga bisani kuma turawa suka gina barikin sojoji a birnin a 1901.[1] Tana daga yammacin yankin kogin Aba, kuma tana daura da titin zuwa jihar Portharcourt, Owerri, Umuahia, Ikot Ekpene, da kuma Ikot-Abasi.[2] Birnin Ta zamo wajen tattara kayan amfanin gona bayan turawa sun samar da titin jirgin kasa wanda ya ratse birnin zuwa birnin Portharcourt. Aba ta kasance birni kuma cibiyar kasuwanci a yanki mai zagaye da kananan kauyuka da birane.

Asalin mutanen Aba sune kabilar Ngwa. Sannan Aba tayi fice ta fuskar kwararrun 'yan siyasa dake cikinta kuma itace birnin da tafi kowace birni tara yawan jama'a a yankin kudu maso gabashin. An ayyana cewa Aba tana da yawan mutane kumanin 2,534,265 a 2016.[3]

Wata kasuwa a Aba

Aba birni ne dake kunshe da kauyuka da dama kamar su; Aba-Ukwu, Eziukwu-Aba, Obuda-Aba and Umuokpoji-Aba amma an hade ta da kauyen Ohazu don samun cigaban gudanarwa. Yankin Aba-Ukwu ba shakka itace yanki mafi muhimmanci a jihar Aba. Anayi wa marigayi Eze W.E Ukaegbu na Aba-Ukwu lakabi da "9th Grand Son of Aba" watau jikan Aba na tara.

Daga bisani ta zama yankin kulawar turawa mulkin mallaka. Aba ta zamo daya daga cikin muhimman cibiyoyin kasuwanci na kasa tun daga lokacin da ta zamo daya daga cikin yankin tsohuwar Gabashin Najeriya.

Yakin tawaye na Aro, na daya daga cikin gumurzu na aniyan korar turawan mulkin mallaka a yankin, wanda ya faru a yankunan Aba a cikin shekarun 1901 da 1902. Turawa sunci galaban inyamurai cikin sauki a yakin kuma ba'a san mutane nawa suka salwanta a yakin ba.[4] A cikin shekara ta 1901, turawa sun kafa barikin sojoji a Aba sannan a cikin shekara ta 1915, sun kara samar da titin jirgin kasa wanda ya wuce zuwa jihar Portharcourt wanda ke sufurin kaya kamar manja da man-kadanya.[2] Acikin shekara ta 1929, Aba na daya daga cikin yankunan tawaye na mata wanda akafi sani a tarihance da "The Aba Women's Riot". Zanga-zanga ne kan harajin turawan mulkin mallaka. Rikicin ya fara ne a matsayin zanga-zanga na laluma da mata suka fara a yankin, wanda daga baya wai akaci matan tara akan hakan. Zanga-zangan ya watsu zuwa sauran kasashen inyamurai amma a matsayin zanga-zangan laluma har zuwa lokacin da aka make wata mata mai ciki a yayinda aka fara wani dan gumurzu wanda a dalilin hakan matan ta rasa jaririnta.[5] Wannan labarin abun bakin cikin ya wanzu zuwa kasashen yankunan inda daga baya ya jawo munanan sakamako. Bayan kashe-kashe da dama, wasu ta kaddara wasu kuma akasin haka, kungiyar mata akalla 10,000 sunyi tattaki a Aba. An sanar da sakamakon mutuwar da aka samu a lokacin tsakanin mutum 55 zuwa 100.[6] Zuwa shekarun 1930s, Aba ta zamo babban gari da manya masana'antu

A daidai tsakiyar yakin basasan Najeriya na 1967, An maido da babban birnin Biafra zuwa Umuahia daga Enugu. Aba ta zamo yankin salon dabarun yakin Biafra a lokacin, kuma an jefa bama-bamai da dama a yankin Biafra.[7]

Aba

Aba gida ne ga fitattun mutane kaman Emejiaka Egbu na iyalin Aba la Ohazu, Ogbonna iyalan Eziukwu-Aba, Ichita na iyalin Umuokpoji-Aba da makamantansu.

Tattalin Arziki

[gyara sashe | gyara masomin]

Aba zagaye take da rijiyoyin mai wanda suka raba ta da birnin Portharcourt. Hanyar sufurin man-fetur (pipeline) mai tsawon kilomitoci 30km (19 mi) ke kawo mai zuwa Aba daga matatan mai na jihar Imo.[8] Daga cikin muhimman arzikin garin shine masaka (textile) da kuma manja, sauran hajoji sun hada da wuraren sarrafa magunguna, robobi, siminti, kayan kwalliya da.[9] dai sauransu. A dalilin haka yasa kasuwa Ariaria International Market ta zamo na daga cikin manyan kasuwannin Najeriya bayan kasuwar Onitsha. Har wayau akwai kamfanin gidan giyan Heineken, kamfanin gilasai, da na sarrafa ruwa duk a cikin Birnin. Tayi fice a sana'oin hannu.[9] and distillery within the city. Finally, it is famous for its handicrafts.[8]

Kafar wutar Lantarki

[gyara sashe | gyara masomin]
Aba

Kamfanin "Enugu Electricity Distribution Company" ke kai wa Aba wutan lantarki, wanda aka samar ta hanyar raba kamfanin wuta na Najeriya. Bugu da kari akwai sabon gidan wuta wanda ake kira Geometric Power Company, idan ya fara aiki zai iya baiwa Aba wuta a koda yaushe.

Birnin ta taka rawa matuka a wajen yaduwar akidar Christian evangelism a kudancin Najeriya tun lokacin da turawa suka kawo makarantar "Church Missionary Society (CMS)", suka kawo motar "Church of England" wanda yanzu suka samar da Anglican Church of Nigeri. Cocin da ake kira All the Saints, ya samo asaline daga malaman Evangelism uku na yankunan safaran mai da suka hada da "Opopo-Joseph Cookey, Gabrial Coookey da kuma Zedekiah Cookeys". Wannan mutane sun biyo ta Azumini Blue River (Kogin Aba) a 1896 don kasuwanci da kuma kafa addinin kiristanci a yankin. A cikin shekara ta 1897, sunyi yarjejeniya da mutanen Abayi da Umuocham akan fili da zasu kafa kasuwancinsu na man fetur a gabar teku na yankin Umuocham da kuma yankin Abayi. Mutanen sun fara sana'arsu na man-fetur wanda daga bisani suka sa mutanen Aba suka amshi addinin Kiristanci. Daga 1901 zuwa musamman 1902 sun gayyaci ubannin gidansu zuwa yankin wanda a dalilin haka aka samar da wuraren bauta, daya a Abayi, daya kuma Umuocham a matsayin sadaukarw ga James Johnson (1900–1917).

An gina cocin St. Michael's Cathedral Anglican Church a 1920s, yawancin cocukan suka samr da makarantun firamare da sakandare na yankin na lokacin.[10]

Malaman kiristoci da suka fara zuwa Najeriya sun zo ne a 1842, kuma suka gina cocin Methodist Church Nigeria a Badagry. Nan da nan ta yadu zuwa Uzuakoli (tafiyar Kilimita 50 daga Aba) da bisani Aba.

Acikin shekara ta 1923, aka gina cocin "Seventh-day Adventist Church (SDA Church)". Cocin na Seventh-day Adventist sunyi fice a fanni tauhidin addinin kiristanci da kuma asibitoci masu inganci.[11]

Suma Catholica sun taka rawa inda suka gina cocin Christ the King Church (C.K.C) wanda shine coci mafi girma a garin har na tsawon lokaci

Zuwan akidar "Pentecostal Christianity" Najeriya ta samu nata kason a Birnin Aba, inda suma suka kafa cocin "Assemblies of God Church", Deeper Christian Life Ministry, Living Word Ministries Inc. sun sama mabiya sosai a 1980s.[12]

Haka zalika akwai musulmai da masallatai a Aba. Masallaci mafi girma a yankin shine masallacin Hospital Road Mosque. Babban limamin bahaushe yana zaune a tsakiyar garin.

Birni na dauke da makarantun firamare akalla guda 90 wanda suke gudana safe da rana a yankin. Makarantun na gudana ne tsakanin lokutan 07:30Hrs – 12:30Hrs and 12:30Hrs – 17:30Hrs na Najeriya.

Makarantun Firamare a Aba
  • Ogbor Hill Primary School
  • Living Word Magnet Schools
  • Aba-Owerri Road Primary School
  • Asa Road Primary School
  • Asa Triangle Primary School
  • Constitution Crescent (Santa Maria) Primary School
  • School Road Primary School Aba
  • Cameroun Barracks Primary School
  • City Primary School
  • Township Primary school
  • Ohabiam Primary School
  • Umuagabai Primary School
  • Golf Course Primary School
  • St Bridget Primary School
  • Abayi Umuocham Primary School
  • Abayi Ariaria Primary School
  • Ndoki Road Primary School
  • Danfodio Road Primary School
  • Ehere Road Primary School
  • Azikiwe Road Primary School
  • Tenant Road Primary School
  • Market Road Primary School
  • Cameroun Road Primary School
  • St. James Model Primary School (private)
  • Hospital Road Primary School
  • Okigwe Road Primary School
  • Omuma Road Primary School
  • College primary School
  • 67 Infantory Battalion Primary School, Umule
  • Living Stone Int'l Christian Primary School, Ogbor-Hill Aba, Abia State
  • Lilac primary school ogbor hil,Aba
  • International Early Learning Centre, Umuodu, Abayi Aba
  • Eagle Height Academy, 56 Cameroon road, Abayi Aba
  • Daughter of Mary Mother of Mercy Primary School - owned by the catholic church, and is among the first five primary school in Aba in the 90s alongside st Bridget and intl early learning.
Makarantun Sakandare a Aba
  • Methodist High School, Park Road Aba
  • Presbyterian Secondary School, Ogbor Hill Aba
  • Living Word Academy Secondary
  • Ngwa High School (NHS) or (NAHISCO)
  • (Ibo) National High School (NACO)
  • Girls' Technical College
  • Sacred Heart College Eziukwu Aba (SAHACO)
  • Eziama High School (Apostolic Grammar School)
  • Wilcox Memorial Comprehensive Secondary School, Ogbor hill Aba
  • All Saints Secondary School, Ehere Aba
  • Community Girls Secondary School
  • Secondary Technical School
  • Nigerian Christian Seminary School
  • Boys Technical College [BTC]
  • Girls High School, Ogbor Hill.
  • Ninlan Demonstration Secondary School.
  • Ovom Girls High School, Ovom
  • Ohabiam Girls Secondary School, Ohabiam.
  • Nneise Community Secondary School, Umuezu.
  • St. Joseph College Aba
  • Iheorji Secondary School Aba
  • Osusu Secondary School Aba
Makarantu masu zaman kansu a Aba
  • Living Word Magnet Schools (Nursery/Primary)
  • Living Word Academy (Secondary)
  • St. James Model School (Hosts JAMB and other graduate exams)
  • Premier International Secondary School
  • New Breed International Schools
  • Evangel Seminary
  • Alberto Model School
  • Dority International Secondary School (Hosts SAT and Toefl Exams for foreign colleges)
  • St Bridget High School
  • St Anthony Comprehensive Secondary School Aba.
  • Living Stone International Christian Secondary School, Ogbor-Hill Aba, Abia State
  • Living Word Academy Secondary, Abayi, Aba.
  • D-nals High school,opobo Rd Aba.
  • Rich Devos International High School, Aba.
  • Presbyterian secondary school, Ehere, Aba.
  • Awesome International Model Secondary School, Abayi Aba.
  • Infotech Demonstration School Aba.
  • stella maris secondary school aba.
  • merit base international Christian school Aba
  • St. Joseph College Aba
  • Intellectual Giants Christian Academy
  • Modern Child College Aba
  • St. Augustine's Model Academy, Ogbor Hill, Aba.
  • Lilac Comprehensive Secondary School, Ogbor Hill, Aba
  • Hawics International School
Jami'oin Aba

The tertiary schools are:

  • Abia State University Teaching Hospital
  • Abia State Polytechnic
  • Covenant Polytechnic
  • School of Health Technology
  • Redemption College of Education (privately owned)
  • Rhema University, Aba Take-off site (also privately owned by Living Word Ministries)
  • Infotech College of Technology (privately owned)
  • Cyberspot Institute of Information Technology (privately owned)
  • Living Word Institute of Information Technology (privately owned)
  • Imo state university extension in nursing school off Mosque Road

Kungiyar wasan kwallon kafa ta Eyimba watau "Enyimba International F.C." wanda akafi sani da The Peoples Elephant, itace fitacciyar kungiyar wasan kwallon kafa a Garin. Nasara kungiyar wasan kwallon kafa na Eyimba tana da tasiri matuga ga wasan kwallon kafa a Najeriya. Suna da kofuna biyu na CAF Champions League, kofuna shida na Nigeria Premier League, da wasu kofunan biyu na Federation Cup. Kungiyar itace ta biyu a cikin jerin kungiyoyin wasan kwallon kafa na "CAF Club Rankings".

Refuse skip at Osisioma Junction
Bola a yankin Osisioma

Akwai matsaloli da dama dangane da shara a birnin Aba wanda suke a dalilin rashin tara bolili da kula dasu wannan na nufin ana zubar da shara cikin rashin kula da yankunan kasuwanni da suka cika garin.[13]

  1. Munro, David, ed. (1995). "Aba". The Oxford Dictionary of the World. Oxford, UK: Oxford University Press. ISBN 0-19-866184-3.
  2. 2.0 2.1 "Hoiberg, Dale H., ed. (2010). "Aba". Encyclopædia Britannica. Vol. I: A-Ak – Bayes (15th ed.). Chicago, Illinois: Encyclopædia Britannica, Inc. ISBN 978-1-59339-837-8.
  3. "Abia (state, Nigeria) - Population". Citypopulation.de. Retrieved 25 July 2016.
  4. "Oriji, John N. (2011). Political Organization in Nigeria since the Late Stone Age: A History of the Igbo People. New York, NY: Palgrave Macmillan. ISBN 978-0-230-62193-0.
  5. "Oriji, John N. (2011). Political Organization in Nigeria since the Late Stone Age: A History of the Igbo People. New York, NY: Palgrave Macmillan. ISBN 978-0-230-62193-0.
  6. "Lemberg, David S.; Courtlandt, Canby (1984). "Encyclopedia of Historical Places". Encyclopedia of Historical Places. Facts on File Library of World History. Vol. 1. New York, NY: Facts on File. ISBN 978-0871961266.
  7. Opia 1972, p. 8
  8. 8.0 8.1 Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named EB
  9. 9.0 9.1 Munro 1995, p. 2
  10. "Aba Religions, Religions in Aba, Religions of Aba :: Traveltill.com". Traveltill. Retrieved 2021-06-18.
  11. General Conference of Seventh-day Adventist 2014
  12. "aba giants". echodiplomatiques.com. Archived from the original on 2021-06-24. Retrieved 2021-06-18.
  13. Izugbara, C. O.; Umoh, J. O. (2004). "Indigenous Waste Management Practices among the Ngwa of Southeastern Nigeria: Some lessons and policy implications". The Environmentalist. 24 (2): 87–92. doi:10.1007/s10669-004-4799-4.