Majalisar Dokokin Jihar Neja

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Majalisar Dokokin Jihar Neja
unicameral legislature (en) Fassara
Bayanai
Ƙasa Najeriya
Applies to jurisdiction (en) Fassara Jihar Neja

Majalisar dokokin jihar Neja ita ce bangaren da ke tsara dokokin gwamnatin jihar Neja ta Najeriya.[1][2][3] Majalisar dokoki ce mai mambobi guda 27 da aka zaba daga kananan hukumomi guda 25 na jihar.An kayyade kananan hukumomin da ke da yawan mabukata a mazabu biyu don ba da wakilci dai-dai. Wannan ya sanya yawan 'yan majalisar a majalisar dokokin jihar Neja sunkai guda 27.

Ayyukan yau da kullun na Majalisar sune ƙirƙirar sabbin dokoki, gyara ko soke dokokin da ke akwai da kuma kula da zartarwa. An zabi membobin majalisar na tsawon shekaru hudu tare da 'yan majalisar tarayya (majalisar dattijai da ta wakilai). Majalisar jihar tana yin taro sau uku a mako (Talata, Laraba da Alhamis) don yin cikakken zama a harabar majalisar a cikin babban birnin jihar, Minna . Ana gudanar da kwamitoci da ayyukan kulawa kamar yadda membobin suka yanke.[4][5][6][7]

Honarabul Abdullahi Wuse da Bako Kassim Alfa a matsayin kakakin majalisa da mataimakin kakakin majalisar. Bako Kasim wanda aka zaba tare da kakakin majalisar a ranar daya ya sauka daga matsayinsa na mataimakin kakakin majalisar tare da wani dalili da ba a bayyana ba, sannan an zabi Jibrin Baba na mazabar Lavun a matsayin mataimakin kakakin majalisar.

Jerin wakilai[gyara sashe | gyara masomin]

  • Ahmed Marafa, mai wakiltar Chanchaga
  • Abdullahi Wuse, mai wakiltar Tafa, Shugaban Majalisar
  • Bako Kassim Alfa,mai wakiltar Bida I
  • Jibrin Ndagi Baba,mai wakiltar Lavun, mataimakin kakakin majalisar
  • Abdullahi Mohammed Kagara (APC), mai wakiltar Raffi,magatakarda,
  • Mohammed Bashir Lokogoma, mai wakiltar Wushishi.
  • Hussaini Ibrahim (APC),mai wakiltar Agaie
  • Isah Ibrahim (APC),shugaban masu rinjaye, mai wakiltar Rijau
  • Musa Alhaji Sule (APC),mai wakiltar Katcha, Babban Bulala
  • Mohammed Abba Bala (APC),mai wakiltar Borgu.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "8th Niger State House of Assembly commences | Newsline Newspaper". www.newsline.org.ng. Archived from the original on 2020-06-25. Retrieved 2020-06-24.
  2. "APC leads Niger Assembly polls". Latest Nigeria News, Nigerian Newspapers, Politics (in Turanci). 2019-03-11. Retrieved 2020-06-24.
  3. Hamagam, From Aliyu M.; Minna (2015-04-12). "Results of 4 LGs for Niger state House of Assembly". Daily Trust (in Turanci). Archived from the original on 2020-06-26. Retrieved 2020-06-24.
  4. "Niger Assembly passes contributory healthcare bill, reinstates suspended member -". The Eagle Online (in Turanci). 2018-12-21. Retrieved 2020-06-24.
  5. "Niger House Of Assembly Passes 2016 Budget, Sustains Pension Scheme". Channels Television. Retrieved 2020-06-24.
  6. "Niger House Of Assembly Confirms Eight Commissioners". Channels Television. Retrieved 2020-06-24.
  7. "Niger Assembly grants Gov. Bello's request for N1.5b Agric loan-". The Eagle Online (in Turanci). 2018-11-27. Retrieved 2020-06-24.