Gundumar Sanatan Neja ta gabas
Gundumar Sanatan Neja ta gabas | |
---|---|
senatorial district of Nigeria (en) | |
Bayanai | |
Ƙasa | Najeriya |
Wuri | |
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya |
Jiha | Jihar Neja |
Gundumar Sanatan Neja ta Gabas wanda aka sani da sashe na biyu a wakilcin siyasar Neja (Zobe B) wannan gunduma tana a cikin jihar Neja Najeriya. Wannan gundumar ta haɗa ƙananan hukumomi guda 9 wanda ya haɗa da:
- Ƙaramar Hukumar Rafi
- Ƙaramar Hukumar Munya
- Ƙaramar Hukumar Bosso
- Ƙaramar Hukumar Chanchaga
- Ƙaramar Hukumar Paiko
- Ƙaramar Hukumar Shiroro
- Ƙaramar Hukumar Suleja
- Ƙaramar Hukumar Tafa
- Ƙaramar Hukumar Gurara.
Har ila yau wannan gundumar tanada ƙananan gundumomi (wards) guda 90, Mohammed Sani Musa na jam'iyyar APC shine wanda yake wakiltar waɗannan Ƙananan hukumomi na jihar Neja ta gabas a Majalisar dattijan Najeriya.[1][2][3]
Jerin Sanatocin da suka wakilci yankin[gyara sashe | gyara masomin]
Sanatoci | Jam'iyya | Shekara | Jamhuriya | Tarihin siyasa |
---|---|---|---|---|
Ibrahim Kuta | PDP | 1999 - 2007 | 4th | |
Dahiru Awaisu Kuta | PDP | 2007 - 2011 | 6th | Ya rasu a lokacin da yake a ofis a shekara ta 2014 |
David Umaru | APC | 2011 2019 | 7th | Kotun ɗaukaka ƙara itace ta tumɓukeshi a jamhuriya ta 9
A watan Nuwamba a 2019, ƴan watanni kaɗan kafin ƙarshen wa'adin shi Lokacin sanatan |
Sani Mohammed Musa | APC | 2019 - Mai ci yanzu | 9th | Sani Mohammed Musa Ya maye gurbin David Umar bayanda kotu ta tumɓuke David Umar |
Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]
- ↑ Olasupo, Abisola (15 February 2019). "Elections may not hold in Niger East, North". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in English). Retrieved 10 January 2022.CS1 maint: unrecognized language (link)
- ↑ "INEC issues certificate of return to Niger East senator-elect - Premium Times Nigeria" (in English). 9 September 2014. Retrieved 10 January 2022.CS1 maint: unrecognized language (link)
- ↑ "Breaking: Supreme Court sacks Niger East senator, announces his replacement -". The Eagle Online (in English). 14 June 2019. Retrieved 10 January 2022.CS1 maint: unrecognized language (link)