Ahmed Marafa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

 

Ahmed Marafa
Rayuwa
Sana'a

Ahmed Mohammed Marafa dan siyasan Najeriya ne wanda aka zabe shi a matsayin shugaban majalisar dokokin jihar Neja karo na 8 a shekarar 2015. An zabi Marafa a matsayin dan majalisar jiha daga Chanchaga a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress APC. yazama jihar neja ne bisa goyon bayan Bashir Lokogoma mai wakiltar mazabar Wushishi, sai Bako Alfa daga mazabar Bida ta Arewa ya mara masa baya.[1] Bayan rantsar da shi,Ahmed Marafa ya ce zai samar da dokoki masu ma'ana da za su daukaka yanayin cigaban jama'ar jihar.[2]

A watan Nuwamban shekarar 2015, aka zabi Marafa a matsayin shugaban kungiyar masu magana da yawun Arewacin Najeriya. kungiyar shuwagabannin majalisun jihohi 19 ne akarkashin sa. A lokacin yakin neman zaben shekarar 2019, Marafa ya sha ba'a da suka daga matasa inda suke rera masa waka mai taken wa'adi daya kawai. Wakar dai na nufin ba sa goyon bayan sake tsayawa takararsa a majalisar dokokin jihar. An kama wasu matasa hudu da ke da hannu a wannan waka tare da gurfanar da su a gaban wata babbar kotun majistare da ake zargi da aikata laifuka uku da suka hada da hada baki da tada hankali.[3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-10-28. Retrieved 2022-10-28.
  2. https://www.shineyoureye.org/person/marafa-ahmed-guni
  3. https://www.sunnewsonline.com/tag/alhaji-ahmed-marafa-guni/