Jump to content

Ahmed ibrahim zakzaky

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Ahmed ibrahim zakzaky (An haife shi a ranar Asabar 13th ga watan Octoba shekarata alif 1990), A unguwar kwarbai dake cikin Birnin Zazzau a jihar Kaduna a tarayyar Najeriya. an fi sanin sa da Sayyid Ahmad Ibrahim yana ɗaya daga cikin ƴaƴan Ibrahim Zakzaky.[1]

Ya fara da karatun gida ne a bangaran karatun Al-Qur'ani da karatukan Fiqihu da fannin Ibadat da Ma'amalat da kuma fannoni dabam-dabam da ake karantawa a zaurukan karatu a cikin Birnin Zariya, wadannan duk a gun mahaifin sa ya karanta su a gida. Ya yi karatunsa na primary a Buk International School dake daura da filin koyan tuqin Jirgin sama na Aviation dake Zaria, daga shekarar 1996 zuwa 2002 Yayi makarantar Thybow International School Zaria daga shekarar 2002 zuwa 2004, daga nan yabari ya koma Zaria Academy daga 2005 zuwa 2007 sai yabar Zaria academy yakoma Holemark har akayi masa double promotion yashiga SS2 maimakon yashiga SS1. Bayan nan yagama Secondary School A shekarar 2009, Amma baisamu wucewa makaranta ba sai a 2011. Ya yi amfani da wannan damar wajan fadada bincike a kan wasu fannoni na karatun sa. A lokaci guda kuma ya sami dama sosai wajan taimakon mahaifin Sa a kan ayyuka na yauda kullum da mahaifin sa Shaikh Ibrahim Zakzaky (h) ya saba gudanarwa domin taimakon Al-umma, kamar tafiye-tafiyen sa da ayyukan gine-ginen cibiyoyin addini dama wasu ayyukan daban. Yasami nasarar wucewa China ne A shekarar 2011, Inda yayi karatunsa na Chemical Engineering . Sayyid Ahmad ya sami cikakkiyar tarbiyya daga mahaifinsa, dan haka ya haifar da ayyuka na musamman da suka zama abin koyi ga yan baya. Tun yana yaro ya yi aiki kafada da kafada fanin tsaro na Harisawan Harkar Musulunci sakamakon cigaban tunanin sa yasa ya kafa rundunar Muassasatu Sayyid Abul Fadalul Abbas (A.S) wannan rundunar bayan kafuwar ta, ta haifar da rassa na fannonin ayyukanta a ciki da wajen harka zuwa sassa dadan-daban.[2]

Shahadar sa

[gyara sashe | gyara masomin]

Ya yi shahada ne a lokacin da ake da Ake gudanar da zanga-zangar lumana a garin Zariya don nemawa al'ummar kasar falasdinu yanchi Wanda ake kira Qudus day a turance a shekarar 2014. Sakamakon harbin da sojoji sukayi masa.[3]

  1. https://www.blueprint.ng/zakzakys-3-sons-buried-as-names-of-slain-others-released/
  2. https://www.vanguardngr.com/2014/07/sheikh-zakzakys-son-10-others-died-nigerian-troops-shiite-muslims-clash/
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-07-29. Retrieved 2021-07-29.