Ibrahim Zakzaky

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Sheick Ibrahim Yaƙub Al-Zakzaky
Sheikh Ibrahim Al-Zakzaky (jagoran ƴan Shi'aa Najeriya.


Suna Sheikh Ibrahim Yaƙub Al-Zakzaky
haihuwa ranar 5 ga Mayu 1953 daidai da 15 Sha'aban 1372
garin zama Gyallesu Zariya
addini Shi'a
iyali mata Zeenat Ibrahim Zakzaky
Ibrahim Zakzaky a shekarar 2013

Ibrahim Yaqub Zakzaky malamin addinin musulunci ne bangaren Shi'a, kuma Dan gwagwarmayar addini. Shi ya kafa kungiyar 'yan uwa musulmi a shekarar 1979, mutanen gari kuma na ce masu tan Shi'a ko 'yan Burazas.

Tarihin Ibrahim Zakzaky[gyara sashe | Gyara masomin]

Anhaifi Ibrahim Al'Zakzaky a garin Zariya na jihar Kaduna Najeriya a ranar 5 ga watan Mayu na shekarar 1953 daidai da (15 Sha'ban 1372 AH). Ya halarci makarantar Allo sannan sai ya wuce makarantar Larabci a (1969-1970), Sai makarantar larabci a garin Kano daga 1971-1976, inda ya samu iliminsa na grade II. Sai kuma jami'ar Ahmadu Bello (ABU) a garin Zariya (1976-1979), inda ya kammala karatun digirin sa a kan ECONOMICS inda ya samu kyakkyawan sakamako. A lokacin karatun sa a jami'a ne Malamin ya zama shugaban kungiyar dalibai Musulmai ta kasa wato (MSSN). Daga bisani kuma ya zama mataimakin shugaban babbar kungiyar ta ksa mai kula da kasashen waje a (1979).

Zakzaky a shekarun 1990 alokacin yana bayani ga yan'uwansa ɗalibai

Dagananne kuma Sheikh Zakzaky ya fara nuna goyon bayansa ga juyin juya halin da akayi a kasar Iran a shekarar 1979. Daganan kuma sai Zakzaky ya tafi kasar ta Iran bayan dawowarsa ne ya zama jagoran kafa kwangilar shi'a a kasar Najeriya. Yaci gaba da yada addinin Rafidanci a kasar har zuwa shekarun 1990 inda ya tara mabiya masu dumbin yawa akasari matasa masu kaunar sharholiya.

Kungiyar Yan'uwa Musulmi Ibrahim Al'zakkzaki ya kafa kungiyar da ake kira Islamic Movement in Nigeria wadda ada ake kira da Muslim brothers ko kuma yan'uwa musulmi a hausance.

Rikice rikicen Kungiyar Yan'uwa Musulmi[gyara sashe | Gyara masomin]

Wannan kungiya ta zakzaky ta sha fama da rikice rikice da rigingimu tun daga farkon kafata har zuwa yanzu. Fitattu daga cikin rikicin da kungiyar ta fuskanta sun hada da wana ya faru a 1998 da kuma na 2014 da na 2015.

Rikicin Yan shi'a na 2014 a Zariya[gyara sashe | Gyara masomin]

A ranar 25 na watan Yuli na shekarar 2014 ne aka samu tashin hankali tsakanin yan kungiyar yn'uwa musulmi mabiya zakzaky da sojojin Najeriya a birnin Zariya inda mutane 35 suka rasa rayukan su ciki harda yayan Ibrahim Zakzaky guda uku. Rikicin da kungiyoyin kare hakkin bil'afama na duniya da dama ciki harda babbar kungiyar kare hakkin bil'adama ta duniya.

Rikicin kungiyar yan'uwa musulmi na 2015[gyara sashe | Gyara masomin]

Hakama a birnin na Zariya ne a shekarar 2015 sakamakon yan kungiyar yan'uwa musulmi mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky sun tare hanyar da babban Hafsan Sojojin Kasar wato Tukur Yusuf Buratai zai wuce a lokacin wata ziyara da yakai birnin na Zariya. Sai sojojin suka bude wuta akan yan Shi'ar wadanda suka tare hanyar. Lamarin da yayi muni sosai inda har yakai ga rushe muhallan ibadar su da ma makabartar mabiya Shi'a din. Sannan daruruwan mabiya kungiyar sun rasa rayukan su. Haka nan dai lamarin yayi sanadiyyar rasa rayukan na hannun daman malam Zakzaky wato Sheikh Muhammad Mahmud Turi da wasu daga yayan jagoran wato Ibrahimu Zakzaky. Shima da kansa Zakzaky da mai ɗakin sa Zanat sun samu munannan raunuka a lokacin tashin hankalin inda daga bisani jami'an tsaro sukayi awon gaba da su kuma har yanzu hukumar kasar ta Najeriya na tsare da su. Saidai kuma yayan kungiyar ta yan'uwa musulmi suna ta gwagwarmaya da yin zanga-zanga a wasu daga biranen kasar domin ganin an sakar masu jagoran nasu. Saidai lamarin na zanga-zangar yana haddasa wadansu tashe tashen hankulan inda har ake samun rasa rayuka. Amma sakamakon zaman wata kotu a kasar wanda tayi a ranan 2 ga Disamba 2016, ta yanke hukuncin umartar hukumar Najeriya da ta gaggauta sakin malam zakzaky da matar sa tare da biyan sa duyyar naira miliyar 50, tare da wadan su kudirorin. A watan Janairu na 2018 ne aka soma jin duriyar malamin inda ya gabatar da wanu takaitaccen jawabi wanda ba'asan ko wanne wajene ba.

Rayuwar Zakzaky ta kashin kai[gyara sashe | Gyara masomin]

Ya Auri matar sa Zeenah Ibrahim, suna da yaya tara tare. Yanzu yayan sa uku suka rage namiji daya da mata biyu. Uku daga yayan Zakzaky sun mutu ne a Zariya rikicin yan shi'a na 2014 yayin da sauran ukun suka mutu suma a rikicin na 2015 .

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]