Jump to content

Aissa Koli

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Aissa Koli
sarauniya

Rayuwa
Haihuwa Daular Kanem-Bornu, unknown value
ƙasa Daular Kanem-Bornu
Mutuwa Daular Kanem-Bornu, 16 century
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Aissa Koli kuma an kiranta da Aisa Kili Ngirmaramma ta kasance sarauniya ce mai karfin iko a daular Kanem–Bornu a shekara ta 1497–1504 zuwa 1563–1570.

Akwa sabani da yawa akan wani lokacine da tayi mulki. Amman dai a tarihin larabawa basu kawo bayani ba kodaya akanta, amman sananne ne cewa bas kulawa da mulkin mata a gurin tattara tarihi na masu mulki, kuma har wayau an san cewa Idris Aloma shine wanda ya gajeta kuma ya kawar da maguzanci ya kawo addinin Muslim. amman a wasu tarihin yankin afrika an kawo tarihinta kamar yanda na sauran mazan yake.

An ruwaito cewa Aissa Koli ya ce ga Ali Gaji Zanani. baban ta yayi mulki na shekara daya, bayan rasuwansa ne aka bayar da kuma mulkin ga dan dangin su mai suna Dunama, shi kuma sai yayi mulkin shekara daya bayan ya gada a gun babanta. kafin mutuwarsa ya bar wasiya cewa a kashe duk wadanda zasuyi gado daga cikin dangin wanda ya karba mulkin a gunsa wato bababn aissa koli kenan, karamin kanin aissa koli mai suna Idris dan shekara biyar, dan uba suke da aissa koli, sai maman shi tasa aka tura shi Bulala da ke chadi a boye dan kada a kashe shi, a dalilin wasiyyan da sarki Dunama ya bada, Aissa ta gaji sarauta ne bayan kashe duka magada maza da'akayi, batare da ta san cewa kaninta na wurin uba na nan a raye ba. A wani majiyar kuma ance ai aissa yar Dunama ce, saboda haka gado tayi a gun ubanta..

Sarauniya aissa tayi mulki ne na tsawan shekara bakwai 7, wanda a lokacin iya wa'adin sarakuna kenan, wanda a lokacinta sarauta bata da tsanantawa sosai akan cewa lallai mutum sai ya nutu zai bada mulki, bayan lokacinta yayi ne aka bata labari akan karamin kaninta cewa yana raye sai tasa aka kira shi ta nada shi a matsayin magajinta kuma mai bata shawara kafin ta bashi mulkin shi

Diddigin bayanai

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Guida Myrl Jackson-Laufer: Women Rulers Throughout the Ages: An Illustrated Guide
  • Women in World History: A Biographical Encyclopedia