Jump to content

Akhumzi Jezile

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Akhumzi Jezile
Rayuwa
Haihuwa Ngcobo (en) Fassara, 15 ga Janairu, 1989
Mutuwa Aliwal North (en) Fassara, 28 ga Afirilu, 2018
Sana'a
Sana'a jarumi
IMDb nm5465545

Akhumzi Jezile (15 Janairu 1989 - 28 Afrilu 2018) an haife shi a Ngcobo, ɗan wasan Afirka ta Kudu ne, mai gabatar da talabijin kuma furodusa.[1] An fi saninsa da kasancewa mai gabatarwa a wasan kwaikwayon talabijin na SABC 1, YOTV kuma ɗan wasan kwaikwayo a cikin jerin wasan kwaikwayo na SABC 1 Tempy Pushas kuma a matsayin "Ngulube" a cikin Themby Phishers.[2] A cikin shekarar 2014, ya sami lambar yabo ta SAFTA a matsayin Mafi kyawun Jarumi mai Tallafawa a cikin Wasan kwaikwayo na TV don wannan rawa daya taka.

Ya rasu ne sakamakon hatsarin mota da suka yi da Siyasanga Kobese da wasu abokansa biyu, tsakanin Maletswai da Komani a hanyarsa ta zuwa Ngcobo domin binne kakarsa.[3]

Rayuwar farko

[gyara sashe | gyara masomin]

An haife shi a ranar 12 ga watan Janairu 1989 kuma ya girma a Gabashin Cape, Mthatha daga baya danginsa sun ƙaura zuwa Johannesburg. Akhumuzi shine ɗan fari a cikin iyali mai yara biyar. Mahaifinsa ya rasu sa’ad da yake ƙarami kuma mahaifiyarsa Zoleka Jezile ta rene shi. Ya halarci makarantar sakandare ta Winile da ke Katlehong.[4]

Daga shekarun 2016 zuwa 2018, shi ne mai watsa shiri na SABC 1 show Fan Base season 4.[5]

Kyaututtuka da zaɓe

[gyara sashe | gyara masomin]

Ya sami lambar yabo ta Golden Horn Award saboda kasancewarsa mafi kyawun ɗan wasan kwaikwayo a Tempy Pushas a cikin shekarar 2014.[4]

Akhumuzi ya mutu ne a wani hatsarin mota da abokansa guda uku da suka haɗa da Thobani Mseleni da Siyasanga Kobese a Aliwal North kusa da Komani.[4][6] An binne shi a makabartar West Park a Johannesburg[7]

  1. "Akhumuzi Jezile". Tvsa.co.za.
  2. "RIP 10 Facts You Probably Didn't Know about Akhumzi Jezile". sistamag.co.za. Archived from the original on 1 June 2019. Retrieved 1 June 2019.
  3. "Sussanne Khan turns Raveena Tandon's first guest on chat show". Times of India. Indiatimes. 3 September 2014. Retrieved 8 September 2014.
  4. 4.0 4.1 4.2 Albert Simiyu (14 May 2019). "Akhumzi Jezile biography: Age, career, and death". briefly.co.za.
  5. Makhubo, Phumla (6 December 2015). "AKHUMZI TO STEP INTO ZULUBOY'S SHOES! - Daily Sun". Daily Sun.
  6. Molife Kumona (28 April 2018). "Renowned television personality Akhumzi Jezile has died at 29". gq.co.za.
  7. "Akhumzi Jezile laid to rest". 5 May 2018. Archived from the original on 27 January 2021. Retrieved 9 March 2024.