Jump to content

Alhaji musa dan kwairo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Alhaji Musa Dan kwairo

Mawaki ne na Hausa, mawakin gargajiya Wanda ya shahara ye fice a kasar hausa, margayi alhaji Musa Dan kwairo ya cigaba da kasancewa cikin mawakan da darajarsu ke dada habbaka a alummar hausawa,girmamawar Bata tsaya iyaka Nan ba domin kuwa manazarta a duniya suna cigaba da amfanuwa da gudummawar da ya baiwa fagen ilimi, musamman farfesoshi da masu bincike akan yaran Hausa a Jami,oin najeriya da Kuma gavannan.

Haihuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An kuma haifi Musa Dan kwairo a shekarar 1907.a garin bakura Wanda ke tsakanin jihar zamfara da sokoto da kimanin kilomita 105 a binciken Wani farfesa Dake Jami,ar Dan fodio, malami Kuma farfesa A.M BUNZA

Takaitaccen tarihin sa[gyara sashe | gyara masomin]

Musa Dan kwairo an haife shi a shekarar 1907

a garin bakura Wanda ke tsakanin jihar zamfara da sokoto da kimanin kilomita 105, daga bakin farfesa malami a Jami,ar Dan fodio malami farfesa A.M BUNZA, sunan mahaifin sa Usman dankwanda ya rayu a garin kaya Karamar hukumar maradun inda yake yima sarkin kaya maradun Waka a fadarsa, mahaifin Dan kwairo da kakansa duk makadan sarkin kayan maradun ne , Dan kwairo tun yana da shekara 6 zuwa 7 ya fara bin mahaifin sa tsangaya waka.bayan rasuwar mahaifin sa ne ragamar kungiyar Waka ta koma hannun yayansa Aliyu kurna, inda yazama mataimakin sa in Ali bayan Nan shine Mai wakiltar sa

Lakabin Dan kwairo[gyara sashe | gyara masomin]

Lakabin ya kuma samo asali ne tun mahaifin sa na Raye Yana da wani yaro acikin masu masa amshi Mai zakin murya sunan sa Dan kwairo, to Musa tunda ya tashi yake kwaikwayon muryar sa ,da babansa yaga ya ita SE yake ce masa Shima Dan kwairo.

Waƙa[gyara sashe | gyara masomin]

Musa Dan kwairo yayiwa sardaunan sokoto Waka ,wakar ga Mai nasara garnakaki sardauna inda yai masa Waka Mai taken Mai dubun nasara garnakaki sardauna, margayi sardauna ya fifita tawagar Dan kwairo akan dukkan mawakan hausa, inda ya Maida Dan kwairo mawakin fadarsa da kyautatawa na wuce misali a wancan lokacin , Dan kwairo yayi sardauna margayi Waka akalla yakai 17, musabbabin saduwarsa da sardauna margayi sardauna Dan siyasa ne basareke Wanda ya ke bukatar mawaki daze dinga masa Waka domin ya dabbaka sunan sa sun hadu a siyasar NPC(Northern people Congress),bayan rasuwar sardauna margayi tawagar Dan kwairo ta Dan kwanta Dama na Wani lokaci Mai tsawo kafin suka dawo Waka ga sarakunan dasuka shahara irinsu su sarkin daura sultan na sokoto sarki aminu na Zaria.

Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Musa ya rasu tsakanin Shekaru 29 zuwa da 34 inda kuma ya rasu yabar Yaya 14 Maza 7 mata 7 da jikoki 104, bayan rasuwar sa sunci gaba da hayayyafa Wanda babban Dan sa Alhaji garba Musa Dan kwairo ya bayyana.

  1. Manazarta
  2. https://hausa.legit.ng/1142406-takaitaccen-tarihin-rayuwar-marigayi-alhaji-musa-dankwairo.html
  3. https://ng.opera.news/ng/en/culture/amp/51ad2c7c58ce1576a7cdf4f8d8c1af34 Archived 2023-07-18 at the Wayback Machine
  4. https://www.last.fm/music/Alhaji+Musa+Dankwairo/+wiki
  5. https://taskarlabarai.com/2021/06/19/takaitaccen-tarihin-makada-alhaji-musa-dankwairo-muradun-1902-1991/ Archived 2023-07-18 at the Wayback Machine
  6. https://www.bbc.com/hausa/labarai-51786861.amp