Jump to content

Alter Date

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Alter Date
Asali
Ƙasar asali Najeriya
Characteristics

Alter Date fim ne na ban dariya na soyayya na Najeriya wanda aka yi a 2019. Marc Adebesin ne ya shirya kuma Yemi Banjoko ne ya bada umarni.[1][2]

Fim din da ya tattauna matsalolin da mata suka fuskanta game da maza sun hada da Iyabo Ojo, Bolanle Ninalowo da Kenneth Okolie.[3]

Fim ɗin ya ta'allaka ne akan abokai guda uku waɗanda ke neman soyayya. Na farko tana buqatar mai kud'i, na biyu kuma, ba sa'a da maza sai na qarshen soyayyar ba ta da wani taimako kuma kullum tana soyayya da mazan da ba su dace ba.[4]

Farko An nuna fim din ne a ranar Laraba, 17 ga Afrilu, 2019, a Cinema Silverbird, Ikeja City Mall, Legas kwanan nan.[4][5]