Jump to content

Amany Ali

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Amany Ali
Rayuwa
Haihuwa 2 ga Maris, 1976 (48 shekaru)
ƙasa Misra
Sana'a
Sana'a powerlifter (en) Fassara

Amany Ali ƴar wasan nakasassu ce Kuma ƴar ƙasar Masar ce.[1] Ta wakilci Masar a wasannin nakasassu na bazara ta shekarar 2012 da kuma a wasannin nakasassu na bazarar shekarar 2016 kuma ta sami lambar tagulla a gasar kilogiram 73 na mata a cikin shekarar 2016.[1]

A gasar cin kofin duniya ta shekarar 2014 ta lashe lambar azurfa a gasar kilo 73 na mata. Ta kuma shiga gasar cin kofin duniya ta shekarar 2019 inda ta ƙare a matsayi na 5 a gasar mata ta kilogiram 86.[2]

A gasar Afrika ta shekarar 2015 ta lashe lambar tagulla a gasar mata ta kilogiram 67 da 73.

A gasar cin kofin duniya ta duniya Para Powerlifting na 2018 ta lashe lambar azurfa a gasar mata ta kilogiram 86.[3]

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Amany Ali at the International Paralympic Committee