AmbondronA (band)
AmbondronA (band) | |
---|---|
musical group (en) | |
Bayanai | |
Farawa | 2001 |
Work period (start) (en) | 2001 |
Nau'in | pop rock (en) |
Shafin yanar gizo | ambondronasite.net |
AmbondronA wani pop rock ne daga Madagascar. Ƙungiyar ta yi fice sosai a fagen kiɗan Malagasy tun a shekarar 2001.[1]
Ambondrona ya zagaya sosai a duk faɗin Madagascar, kuma ya yi wasanni da yawa a cikin tsibirin tekun Indiya, Faransa da Afirka ta Kudu. [2] Ƙungiyar ta fitar da albam shida.[3]
A cikin shekarar 2012, Ofishin Jakadancin Amurka a Antananarivo ya zaɓi membobin ƙungiyar don shiga cikin Shirin Jagorancin baƙi na duniya kan taken "Kare Muhalli ta hanyar kiɗa." nadin nasu ya biyo bayan hadin gwiwa ne da Ma'aikatar harkokin Wajen Amurka inda Ambondrona ya dauki hoton bidiyon waka a gandun dajin na Ranomafana tare da inganta kiyaye muhalli da yawon bude ido a Madagascar.[1] A matsayin wani ɓangare na Shirin Jagorancin baƙi na Ƙasashen duniya, ƙungiyar ta yi aiki a biranen Amurka da dama, ciki har da Denver, Colorado da Portland, Oregon.
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]- Music of Madagascar
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 "AmbondronA: Site Officiel" (in French). AmbondronA. 2009. Archived from the original on 6 March 2012. Retrieved 22 April 2013.
- ↑ "AmbondronA, Madagascar's award-winning pop/rock band at IFCC". World Affairs Council of Oregon. 24 July 2012. Archived from the original on 4 March 2016. Retrieved 22 April 2013."AmbondronA, Madagascar's award- winning pop/rock band at IFCC" . World Affairs Council of Oregon. 24 July 2012. Archived from the original on 4 March 2016. Retrieved 22 April 2013.
- ↑ Mahetsaka (21 February 2013). "Un nouvel exploit pour le groupe de Pop rock AmbondronA" (in French). Midi Madagasikara. Archived from the original on 2013-02-24. Retrieved 22 April 2013.