Annasif Døhlen
Appearance
|
| |
| Rayuwa | |
| Haihuwa | Stavanger, 23 ga Yuni, 1930 |
| ƙasa | Norway |
| Mutuwa | Oslo, 5 ga Janairu, 2021 |
| Ƴan uwa | |
| Mahaifiya | Aimée Collett Bang Døhlen |
| Sana'a | |
| Sana'a | Mai sassakawa |
| Kyaututtuka |
gani
|
Annasif Døhlen (Haihuwa: 23 ga watan Yuni, 1930 - 5 Janairu 2021) ya kasance mai zane-zane na Norway.
Tarihin rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haife ta a Stavanger a ranar 23 ga Yuni 1930, Døhlen 'yar mai zane-zane Aimée Døhlen da Herman Døhlen ce.
Daga cikin ayyukanta akwai hotuna na Johan Scharffenberg, Håkon Bleken da David Monrad Johansen, da kuma siffar Olav V na Norway, Skiglede, wanda aka sanya a Filin wasan kankara na Holmenkollen. Sauran siffofin jama'a sune Ikaros daga 1967 a Bygdøy, Oslo, wani mutum-mutumi na Vangsgutane, wanda aka haifa a Todalen, Møre, da Plankbærarn a Hommelvik, daga 1999. Tana da wakilci a cikin National Gallery of Norway da Riksgalleriet .
Mutuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Ta mutu a Oslo a ranar 5 ga Janairun 2021.