Jump to content

Asabe Madaki

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Asabe Madaki
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Sana'a
Sana'a jarumi
IMDb nm11922570

Asabe Madaki mai hazaka ce wacce ta kasance mai wasan kwaikwayo a bangarorin biyu, Arewa da Kudu, ma'ana masana'antar fina-finai ta Kannywood da kuma masana'antar fina-finan Nollywood, sannan mawakiya ce, baya ga sana'ar daukar hoto da take.[1]

Farkon rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Asabe an haife ta kuma ta girma a cikin garin Kaduna, dake yankin arewa maso yammacin Najeriya, yanzu haka tana zama tare da iyalinta.[2] Asabe tayi makarantar firamare da sakandare ne a kasar mahaifinta sannan ta tafi kasar waje don karatun digirin digirgir sannan tayi karatun Law a jami'ar Scotland.

Asabe Madaki ta kuma dawo gida Najeriya Bayan ta kammala karatunta daga kasar Scotland sannan ta shiga masana'antar kannywood da masana'antar nollywood a shekarar 2015.[3]

Asabe ta yiwa kanta kwalliya a masana'antar kannywood da Fina-Finan Turanci, Asabe tana da burin yin fim Tun daga yarinta kuma yawancin fina-finan Harshen Hausa ne suka ba ta kwarin gwiwa.

  1. https://www.blueprint.ng/at-kannywood-we-promote-tribal-religious-harmony-asabe-madaki/
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-10. Retrieved 2023-07-10.
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-10. Retrieved 2023-07-10.