Jump to content

Asibitin Koyarwa na Jami'a (Lusaka, Zambiya)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Asibitin Koyarwa na Jami'a
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaZambiya
Province of Zambia (en) FassaraLusaka Province (en) Fassara
BirniLusaka
Coordinates 15°25′55″S 28°18′49″E / 15.43207°S 28.31367°E / -15.43207; 28.31367
Map
History and use
Opening1934
Offical website

Asibitin Koyarwa na Jami'a (UTH) tsohon asibitin birnin Lusaka ne, kuma shine babban asibitin jama'a a Lusakan, a ƙasar Zambia. Shi ne asibiti mafi girma da gadaje 1,655.[1] Asibitin koyarwa ne, don haka, ana amfani da shi don horar da ɗaliban koyan aikin likitanci na gida a ƙasar, ma'aikatan jinya da ma sauran ƙwararrun ma'aikatan kiwon lafiya. UTH ita ce babbar cibiyar horar da likitoci a Zambia don likitoci, ma'aikatan jinya, jami'an asibiti da sauran kwararrun a fannin kiwon lafiya. Asibitin na bayar da kulawa ta farko, da sauran nau'o'in agaji matakai daban-daban.

Tarihin Asibitin Koyarwa na Jami'ar

[gyara sashe | gyara masomin]

An gina asibitin a shekara ta 1910 tare da gadaje 15 a lokacin, kuma an yi shi ne don marasa lafiya na Afirka waɗanda mazaje ke kula da su kawai saboda asibitin ba shi da likitoci da ma'aikatan jinya, a wancan lokaci.[2][3] Tare da yanke shawarar matsar da babban birnin ƙasar daga Livingstone zuwa tsakiyar Lusaka, an shirya shirye-shiryen wani babban asibiti don kula da karuwar marasa lafiya. Saboda haka, an fara sabon asibiti a halin yanzu UTH site-(wani ɓangare na asibitin) a cikin 1934 kuma ya zama asibitin horo a wannan shekarar.[4] UTH tana bayar da kulawa ga marasa lafiya da marasa lafiya na kowanne rashin lafiya, kuma cibiyar ce ta masu neman kwararru daga ko'ina cikin ƙasar.[5]

Asibitin da ake takaita sunansa da UTH yana a Lusaka, babban birnin ƙasar Zambiya, kusan nisan kilomita 4 daga gabas da tsakiyar birnin.[6][7]

Fitattun likitoci da malamai

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Christine Kaseba, likitar fiɗa ƙwararriyar likitan mata da mata, tsohuwar uwargidan shugaban ƙasar Zambia (2011-2014)[8]
  • John S. Kachimba, wani mai kula da lafiya kuma mai ba da shawara ga likitan urologist wanda shine babban editan jaridar Medical Journal of Zambia.[9][10]
  • Aaron Mujajati, ƙwararren likita a fannin likitancin ciki.
  1. "Mordernisation | The University Teaching Hospital". www.uth.gov.zm. Retrieved 2020-05-25.
  2. "UTH modernisation: From general to specialist – Zambia Daily Mail". www.daily-mail.co.zm. 3 May 2016. Retrieved 2021-05-19.
  3. "Mordernisation | The University Teaching Hospital". www.uth.gov.zm. Retrieved 2022-05-27.
  4. "Mordernisation | The University Teaching Hospital". www.uth.gov.zm. Retrieved 2020-05-25.
  5. University Teaching Hospital Archived 2012-06-26 at the Wayback Machine ZambianDoctors.com
  6. "Health training | ZUKHWA". www.zukhwa.ed.ac.uk (in Turanci). Retrieved 2021-05-19.
  7. "University Teaching Hospital, Lusaka | ZUKHWA". www.zukhwa.ed.ac.uk. Retrieved 2022-05-27.
  8. Zulu, Delphine (2016-08-16). "Zambia: Kaseba in". Times of Zambia (AllAfrica.com). Retrieved 2016-08-21.
  9. "About MJZ". Zambia Medical Association. Archived from the original on 2 February 2017. Retrieved 30 January 2017.
  10. "Chinese hospital heals sore spot in Zambia". the Guardian (in Turanci). 2013-04-29. Retrieved 2022-11-22.