Auwalu Uba
Rayuwar sa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi farfesa Auwalu Uba ne a shekarar 1964 miladiya 18 ga watan Fabrairu, a garin Hardawa wanda yakƙ garamar hukumar Misau na Jihar Bauchi ƙ gasan Najeriya. Wanda yanzu yana zaune ne ƙ gasar ta Najeriya a garin na Bauchƙ garamar Hukumar Misau.
Karatun sa
[gyara sashe | gyara masomin]Ya fara karatu a Makarantar Central primary school Hardawa a shekarar 1972 zuwa 1978 sannan ya tafi zuwa Government School Misau daga shekarar 1978 zuwa 1982, Daga nan ne yasamu takardar chanjin makaranta zuwa Government Science Secondary School Azare a shekarar 1982 kuma a nanne ya kammala karatun sakandari a shekarar 1983.
Farfesa yayi makarantar Basic Studies (SBS) Ta Zaria daga shekarar 1983 zuwa 1984; Sa'annan yasamu Damar shiga Makarantar ta Ahmadu Bello University Zaria, A bangaren kimiyya na Karatun ƙananun Halittu (Microbiology). Kuma ya kammala digirin sane a shekarar 1987.[1]
Yayi Bautan ƙasar sane a General Hospital Katsina, na Garin Kastina a Najeriya, yayi Digiri na biyu (Masters) a University na Maiduguri a shekarar 1992, Sannan kuma yayi PHD a Medical Microbiology a shekarar 2004 a Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa.
Ya cigaba da ziyartar wadansu manazarta a Jami'ar Wales, Swansea a Engila daga shekarar 2000 zuwa 2001, Ya fara matakinsa na matsayin Graduate Assistants a shekarar 1989 tare da jami'ar Maiduguri, A watan Yuli na shekarar 1995 ya fara aiki a Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa Bauchi a matsayin Lakchara 2,
Ya zama lakchara 1 a shekarar1998 sannan kuma ya zama Associate Farfesa a shekarar 2004 sannan kuma ya zama Farfesa a shekarar 2007.
Sanan daga nan ne ya samu damar zama Vice chancellor a Jami'ar Jihar Bauchi mai suna BASUG.
Kuma mamba ne a American Society of Microbiology, Applied Microbiology na United Kingdom da kuma Nigerian society of Microbiology.
Aikin sa
[gyara sashe | gyara masomin]Farfesa Ma'aikacin gwamnatine a fannin koyarwa wanda yakai matakin farfesa a bangaren (Microbiology)
Kuma ya riƙe mastayi daban daban a gwamnati[2]
Matakan da ya riƙe A Jami'a
[gyara sashe | gyara masomin]- Mai Kula da Jarabawa (Exams Officer)
- Mamba (Departmental post graduate committee)
- Mamba (Student welfare Board A.T.B.U)
- Mamba (University Senate A.T.B.U)
- Mamba (Senate exams misconduct committee A.T.B.U)
- Shugaban kula da Dalibai (Dean Student Affairs)
- Shugaban Dept (HOD Biological science)
- Darecta a (Endowment) A.T.B.U
- VICE CHANCELLOR BASUG
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 ="https://arewaaffairs.blogspot.com/2017/12/profile-of-new-vc-of-basug-prof-auwal.html?m=1">https://arewaaffairs.blogspot.com/2017/12/profile-of-new-vc-of-basug-prof-auwal.html?m=1 Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":0" defined multiple times with different content - ↑ https://africaprimenews.com/2021/11/prof-auwal-uba-bags-award-for-excellence-as-bauchi-state-univ-emerges-centre-of-excellence/?amp=1