Jump to content

Babban jami'in kula da zafi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Babban jami'in kula da zafi
civil servant (en) Fassara

Babban jami'in kula da zafi, ko CHO, ma'aikacin gwamnati ne na birni, wanda ke mai da hankali kan yaƙar hatsarori na matsanancin zafi, da rage tasirin tsibiran zafi.

Yawancin manyan jami'an kula da zafi ana ɗaukar hayar garuruwa, gundumomi, da sauran nau'ikan ƙananan hukumomi. Matsayin ya bayyana a farkon 2020s, tare da birane da yawa acikin yanayi mai zafi suna naɗa manyan jami'an zafi don ƙoƙarin rage tasirin canjin yanayi ta hanyar ƙara inuwa, samar da cibiyoyin sanyaya, dasa bishiyoyi, da dai-daita ayyukan hana zafi. An ƙirƙiri muƙamin jami'in zafi na farko a Los Angeles, gundumar Miami-Dade, Melbourne, Athens, da Freetown. Cibiyar Resilience Foundation ta Majalisar Atlantika Adrienne Arsht - Rockefeller Foundation ce ta shirya yunƙurin ƙirƙirar mukaman.

Eleni Myrivili ita ce babban jami'in kula da zafi na Shirin Matsugunan Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya na yanzu kuma Babban Jami'in Resilience na birnin Athens.