Bahir Dar Kenema Kulab ɗin ƙwallon ƙafa
Bahir Dar Kenema Kulab ɗin ƙwallon ƙafa | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | ƙungiyar ƙwallon ƙafa |
Ƙasa | Habasha |
Mulki | |
Hedkwata | Baher Dar |
bahirdarkfc.com |
Bahir Dar Kenema Football Club (Amharic :Bahardar da kema Kulab ɗin ƙwallon ƙafa) ana kuma kiransa da Bahir Dar City, Kulab ɗin kasan Habasha ne dake birnin Bahir Dar. Suna taka leda a gasar firimiya ta Habasha, babban rukuni na ƙwallon ƙafa a Habasha.
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]An kafa Bahir Dar Kenema a shekarar 1973 a birnin Bahir Dar.
Bahir Dar ta samu kyakyawan matsayi a kakar wasa ta 2017-2018 tana jagorantar rukunin A na babbar gasar Habasha da maki 31 bayan mako na 14.
A ranar 29 ga watan Yulin 2018 kungiyar ta samu nasarar shiga gasar firimiya ta kasar Habasha a karon farko a tarihinta bayan da ta doke kungiyar Inshora ta Habasha Nasarar ta tabbatar mata da matsayi na daya a rukunin A a gasar Higher League ta Habasha (a mataki na biyu) da saura wasanni uku. a kakar wasa ta 2017-18, ta hanyar tabbatar da matsayinsu a cikin babban lig a kakar wasa ta gaba.
A ranar 6 ga watan Agusta 2018 kungiyar ta sanar da tsawaita kwantiragin Paulos Getachew har zuwa kakar wasa ta 2018-19.
Filin wasa
[gyara sashe | gyara masomin]Bahir Dar Kenema sun buga wasansu na gida a filin wasa na Bahir Dar International Stadium . Sun raba filin wasan da Amhara Weha Sera, wani kulob da ke Bahir Dar.
Taimako
[gyara sashe | gyara masomin]Bahir Dar Kenema na da dumbin magoya baya inda magoya bayan kungiyar ke yawan tafiya tare da kungiyar a lokacin wasannin waje.
Sassan
[gyara sashe | gyara masomin]Sassan Ayyuka
[gyara sashe | gyara masomin]- Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata
'Yan wasa
[gyara sashe | gyara masomin]Tawagar farko
[gyara sashe | gyara masomin]Tun daga Maris 7, 2021
|
|
Jami'an kulab
[gyara sashe | gyara masomin]Ma'aikatan Koyarwa
[gyara sashe | gyara masomin]Har zuwa Maris 7, 2021
Manaja/Babban Koci:</img> Fasil Tekalegn
Mataimakin Koci:</img> Tedesse Tilahun