Jump to content

Bala muhammad mande

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Kanar Bala Mohammed Mandetsohon Gwamnan mulkin soja ne a jihar Nasarawa. Daga baya aka nada shi Ministan Muhalli a Majalisar Zartarwar lokaci Shugaba Olusegun Obasanjo.

Farkon Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]
An nada shi a matsayin shugaban mulkin soja na jihar Nasarawa daga watan Yuni 1998 zuwa Mayu 1999 a zamanin mulkin Janar Abdulsalami Abubakar, inda ya mika wa zababben gwamna Abdullahi Adamu a Bayan dawowar mulkin dimokuradiyya.[1]

Takarar Gwamna

[gyara sashe | gyara masomin]
Ya tsaya takarar gwamnan jihar Zamfara a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party(PDP) a 2003, amma ya sha kaye a hannun Ahmad Sani na jam’iyyar All Nigeria People’s Party (ANPP).[2]
An nada Mande a matsayin Ministan Muhalli a Majalisar Ministocin Shugaba Olusegun Obasanjo a watan Yulin 2003, ya rike da mukamin har zuwa watan Yunin 2005.[3]
  1. Bala Mohammed Mande
  2. https://platinumpost.ng/2023/04/07/bala-mohammed-mande-biography-family-education-career-and-net-worth/
  3. https://citizensciencenigeria.org/public-offices/persons/bala-mohammed-mande