Jump to content

Barkono

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Barkono
Scientific classification

Bell Pepper
furen barkono
Cikin burkonu

Barkono tsirrai ne acikin kayan lambu ko kayan Gwari yana cikin kayan hadi na abinci da ake amfani da shi na yau da kullum.

Asalin kalmar

[gyara sashe | gyara masomin]
Koran barkono

Barkono kalmace wadda ake amfani da ita domin Sarrafa harshe da kuma iya amfani dashi kan ita kalmar ta rabu gidaje da dama. Kamarsu:

  • Suna da
  • siffatau

Sashen suna

[gyara sashe | gyara masomin]

Barkono sunane wanda ake amfani dashi ga wani kalar tsiro na kayan gona da lambu yanada kyawon fitowa musamman a kan kyakkyawar kasa irinsu Jigawa da kuma jangargari.

Yankakken barkono kenan

Ana noma shi mafiyawanci don samun kudi kasancewarsa mai amfani wurin dadin dandanon abinci yana da tururi da zafi idan ka ci shi da yawa a abinci ko kuma ba hadin sirki amma yana da dadin dandano da gyara abincin alfarma.

Ana amfani da barkono a cikin misalai dake iya zuwa a cikin jimla domin siffanta wani abu mai ban al'ajabi da kuma rashin tabbas na dabi'u domin a nuna zarra ko kuma kwazo misali.

  • Yanada zafi kamar barkono

Shi kamar barkono yake a ido

  • Banbanci tsakanin wuta da 'barkono kana kuma yana zuwa a cikin sigar karin magana misali
  • Barkono a shaka da dadi amma a jika da kukan tausai