Bibata Ouédraogo
Bibata Ouédraogo | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Burkina Faso |
Karatu | |
Harsuna | Faransanci |
Sana'a | |
Sana'a | Mai kare hakkin mata, gwagwarmaya da mai karantarwa |
Bibata Ouédraogo 'yar Burkinabe ce, mai fafutukar kare hakkin mata kuma tsohuwar malamar makaranta. [1]
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Ta shahara da kokarinta na inganta hakokin jima'i da haihuwa da kuma hakkin kula da lafiyar mata masu juna biyu a Burkina Faso. [2] Ta kuma gudanar da bincike da wayar da kan jama'a game da yaki da cutar kanjamau, kuma ta kasance mai fafutukar yaki da wariyar jinsi da auren ƙananan yara. [3] [4]
A halin yanzu tana riƙe da muƙamin shugabar kungiyar AFDEB reshen Ouahigouya wacce kungiya ce ta mata don ci gaban Burkina Faso. Ta kuma yi aiki a matsayin malama kuma ta yi ritaya daga koyarwa a shekarar 2013. [5] Ta ci gaba da kokarinta na jin kai da fafutuka ko da bayan ta yi ritaya daga koyarwa.
A watan Agusta 2021, an sanya ta a matsayin ɗaya daga cikin mata bakwai masu fafutuka na Afirka waɗanda suka cancanci muƙalar Wikipedia ta Global Citizen, ƙungiyar ƙasa da ƙasa da ƙungiyar bayar da shawarwari. [2]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "My Body My Rights Burkina Faso". www.amnesty.org (in Turanci). Retrieved 2021-08-10.
- ↑ 2.0 2.1 "7 Notable African Women Activists Who Deserve Wikipedia Pages". Global Citizen (in Turanci). Retrieved 2021-08-10. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":0" defined multiple times with different content - ↑ "Burkina Faso: child marriage puts thousands of girls at grave risk". www.amnesty.org.uk. Retrieved 2021-08-10.
- ↑ "The women driving change in Burkina Faso". www.amnesty.org.uk. Retrieved 2021-08-10.
- ↑ Hernández, Hortensia (2016-06-01). "Equal rights for women worldwide: Bibata Ouédraogo". Equal rights for women worldwide. Retrieved 2021-08-10.