Jump to content

Bikin Addae Tuntum

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentBikin Addae Tuntum
Iri biki
Wuri Kukuom, Yankin Ahafo
Ƙasa Ghana

Bikin Addae Tuntum (Akwasidae Tuntum) wani biki ne na shekara-shekara da sarakuna da al'ummar Kukuom-Asunafo da ke yankin Ahafo da ke a da yankin Brong Ahafo na kasar Ghana ke gudanar da shi a duk shekara.[1] Akan yi bikin ne a watan Janairu[2] ko kuma a watan Disamba.[3]

A lokacin bikin, ana maraba baƙi don raba abinci da abin sha. Mutanen sun sanya kayan gargajiya kuma akwai durbar na sarakuna. Akwai kuma raye-raye da buge-buge.[4]

Ana gudanar da wannan biki ne domin tunawa da yakin Ebirimoro tsakanin Sefwis da Ahafos a karni na goma sha takwas 18.[3] Ana kuma gudanar da wannan biki ne domin sake jaddada aniyar mutane a wajan sarkinsu.[5]

  1. "Brong Ahafo Region still feeding the nation". Graphic Online (in Turanci). Retrieved 2020-08-23.
  2. "Festivals Ghana - Easy Track Ghana". www.easytrackghana.com. Retrieved 2020-08-23.
  3. 3.0 3.1 "Akwasidae Tuntum Festival". www.blastours.com. Archived from the original on 2018-05-20. Retrieved 2020-08-23.
  4. "Major Festivals". www.ghanaembassyiran.com. Retrieved 2020-08-21.
  5. "The Consulate General Of The Republic of GHANA in The United Arab Emirates (Dubai)". www.ghanaconsulatedubai.com. Archived from the original on 2020-08-15. Retrieved 2020-08-21.