Jump to content

Bikin littafai da fasaha na Kaduna

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Bikin Littattafai da Fasaha na Kaduna, wanda aka fi sani da KABAFEST, taron adabi da al’adu da fasaha ne na shekara-shekara a jihar Kaduna, Najeriya wanda ya gudana a karon farko a watan Yulin shekarar 2017.[1] Gidauniyar Book Buzz ce ta shirya shi, wanda kuma ke shirya bikin Aké Arts and Book Festival, tare da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Kaduna da Cibiyar Gusau. Haka kuma shi ne bikin littafi na farko da ake yi duk shekara a arewacin Najeriya.[2]