Bill (footballer, born 1978)
Alessandro Faria (an haife shi a ranar 7 ga watan Yuni 1978), wanda aka fi sani da Bill, tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne wanda yake taka leda a matsayin ɗan wasan gaba. An haife shi kuma ya girma a Brazil, ya zama naturalized kuma yana taka leda a tawagar kasar Togo. [1]
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]BSV Schwarz-Weiß Rehden ya sanya hannu a cikin watan Nuwamba 2007,[2] kuma ya koma Brazil a Oeste de Chapecó a cikin watan Satumba 2008. [3]
Ayyukan kasa da kasa
[gyara sashe | gyara masomin]Bill ya fara buga wasansa na farko na tawagar kasar Togo a ranar 8 ga watan Yuni, 2003, a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin kasashen Afrika a shekarar 2004 da Cape Verde, a Lomé. A wannan rana Les Eperviers (laƙabin da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Togo) ta ci 5-2 kuma ya ci ɗaya daga cikin kwallayen da Togo taci.[4] Bill kuma ya buga wa Togo wasa da kungiyar Asante Kotoko ta Ghana a wasan sada zumunci a ranar 29 ga watan Yuni 2003 a Stade de Kégué, Lomé.[5]
Kwallayen kasa da kasa
[gyara sashe | gyara masomin]# | Kwanan wata | Wuri | Abokin hamayya | Ci | Sakamako | Gasa |
---|---|---|---|---|---|---|
1 | 8 ga Yuni 2003 | Stade de Kegué, Lomé, Togo | </img> Cape Verde | 1 - 0 | 5 – 2 | Wasan cancantar shiga gasar cin kofin Afrika na 2004 |
2 | 22 ga Yuni 2003 | Stade de Kegué, Lomé, Togo | </img> Kenya | 1 - 0 | 2 – 0 | Wasan cancantar shiga gasar cin kofin Afrika na 2004 |
3 | 22 ga Yuni 2003 | Stade de Kegué, Lomé, Togo | </img> Kenya | 2 – 0 | 2 – 0 | Wasan cancantar shiga gasar cin kofin Afrika na 2004 |
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Samba mix inspires Togo" . BBC Sport. 23 June 2003. Retrieved 23 June 2003.
- ↑ CBF 2007 transfer list Archived 2009-01-31 at the Wayback Machine
- ↑ CBF 2008 transfer list Archived 2010-05-29 at the Wayback Machine
- ↑ "International Matches 2003 - Africa" . RSSSF. Retrieved 22 May 2018.
- ↑ "Search results" . google.com . [better source needed ]