Bukin Suna a al'ummar Hausawa
Bukin Suna a Al’ummar Hausawa Kamar yadda sunan ya nuna, bukin suna wani yanayi ne da ake hada 'yan uwa da abokan arziki a ci a sha, kuma a yi annashuwa da raha. Ana aiwatar da bukin suna ne idan ranar da aka haifi jaririn ta zagayo; ma'ana bayan mako guda. Ranar suna, rana ce da za a radawa jaririn da aka haifa sunan da za a rika kiran sa da shi.[1]
Galibi
[gyara sashe | gyara masomin]Galibi akasar Hausa ana sanar da 'yan 'uwa da abokan arziki tun ana gobe za a yi sunan domin su hadu musammman da safe domin gudanar da wannan al'ada. Ita ma wannan al‟adar ta yi rauni a halin yanzu, saboda tasirin addinin Musulunci da mafi yawan al'ummar yankin ke bi.
A ranar suna, ana yanka rago a raba goro, liman ya yi wa jariri huduba galibi bayan kwana bakwai da haihuwa, duk da yake ana iya huduba tun ranar da aka haifi jinjiri a radawa yaro suna sai dai ba za a bayyana sunan ba sai ranar suna. Galibi da yake Hausawa mabiya addinin Musulunci ne, don haka, ana zanen sunan ne daga cikin sunayen addinin Musulunci.
Ra`ayoyi
[gyara sashe | gyara masomin]- Ranar radin suna, za a taru tsakanin dangin mai haihuwa da mijinta. Idan wadanda duk ake jira sun taho, za a raba goro ga jama‟a inda za a fara fitar da na malamai da wanzamai da mata . Daga nan sai liman ya yi wa abin haihuwar addu'a da ita kanta mahaifiyar da uban da sauran jama'a baki daya. Yahaya da wasu (2001:99)
- Shi kuwa Gusau (2012:42) Yana da ra'ayin cewa: Zanen suna ko radin suna ana gudanar da shi ga abin da aka haifa, bayan mako daya da haihuwa. Zanen suna ko radin suna ya kasu kashi biyu, akwai zanen suna a gargajiyance, akwai kuma zanen suna a addinance.[2]
- Ta kowace fuska dai za a fahinci bukin zanen suna yana haddasa haduwar dangin mace da na namiji wuri daya domin taya juna murnar samun karuwa ta haihuwar da aka samu. Haihuwa abu ce mai matukar muhimmanci ga Bahaushe. Wannan ne ma ya sa yake girmama duk wata al'ada da ta shafi haihuwa tun daga goyon ciki da haihuwar da kuma renon abin da aka haifa.bShagulgulan suna sukan fara ne da zarar aka ce mace ta haihu a gidan Bahaushe. Wannan ne ya sa Garba (2012:36) yake ganin cewa “ Al’adun bukin haihuwa ko zanen suna al’adu ne da Hausawa ke gudanarwa a lokacin da mace ta haihu har zuwa ranar da aka rada wa abin da aka haifa suna” Saboda haka, shagulgulan bukin suna sun fi kankama ne a ranar da abin da aka haifa ya cika mako ko sati daya da haihuwa.[3]
- Kafin ranar bukin suna akwai al'adun da suka kebanta ga mata kamar gudar sanar da haihuwa da lugude da karar biki da gashin cibi da wankan jego ga mai haihuwa da shan kunun biki da kayar barka (wanda maigida kan tanada) da kuma kayan gara. Dangane da haka, bukin suna ana aiwatar da shi a kasar Hausa bayan sati daya da haihuwar jinjiri domin a sanar da jama'a irin sunan da aka yi masa, wanda ake yi lakabi masa da sunan yanka. A lokacin bukin sunan akan yanka rago, tumkiya, Awaki, a wasu lokuta har ma da shanu ga masu halin yin hakan. Ana aiwatar da wannan yankan ne domin a tabbatar wa jama'a tushe da asalin abin da aka haifa, ma'ana ba shege ba ne.[4]
Irin wannan taron bukin ne ake samar da cikakken suna ga jinjiri. Don haka, duk wani suna na lakabi wanda ake kiran sa da shi kafin ranar suna kamar sunan ranar haihuwa misali Danlali, Danlami, ko Danjumma da sauransu, ko sunayen yanayin halittarsa misali kamar Jatau, Duna ko Cindo da sauransu, za a musanya shi da sunansa na yanka wandaaka samar masa a ranar bukin suna. Sunan yanka yakan iya daukar Muhammadu, Aliyu, usmanu, Abdullahi da sauransu.
Haihuwa da Tanade-tanaden Kayan bukin Suna
[gyara sashe | gyara masomin]A bisa tsarin al'adun Hausawa, akwai tanade-tanaden da mazaje magidanta kan yi domin tarbon abin da za a iya haifa masu da zararr mutum ya fahimci cewa matarsa ta sami juna biyu. Daga cikin irin kayan da ake tanada kuwa sun hada da;
Magungunan Dauri
[gyara sashe | gyara masomin]Wadannan magunguna ne da miji ke tanadar wa matarsa ko kuma iyayen miji ko na matar su tanada domin bai wa mai juna biyu ta sha musamman idan cikin ya kai kimanin wata bakwai zuwa haihuwa. Amfanin magungunan shi ne domin ta sami saukin haihuwa. Magungunan za su wanke zabi da maikon da ke cikin ciki na mai juna biyu, wanda hakan zai sanya ta sami sau}in na}uda a lokacin haihuwa.
Itacen Biki
[gyara sashe | gyara masomin]Maigida zai fara tanadin itatuwan da za a yi amfani da su a wajen shagulgulan wankan jego har zuwa bukin suna da kuma kwanakin da mai jego za ta yi tana wankan rowan zafi.
Kayan Barka
[gyara sashe | gyara masomin]Wadannan kayayyaki ne da suka danganci suturar maijego da abin da ta haifa. Maigida zai tanade su ne tun kafin a haihu ko kuma bayan an haihu. Daga cikin kayan akwai turamen atamfa da kayan jinjirai da turare da man shafi da kitso da sauransu da dama gwargwadon halin magidanci. Al’adun da ke tattare da bukin sunan Hausawa Wadannan al'adu ne da suka shafi shagulgulan da ake yi a ranar suna. Wadannan al'adun kuwa sun hada da;
Taron Suna
[gyara sashe | gyara masomin]Taro ne da 'yan 'uwa da abokanin arziki inda za su taru domin taya murna ga mahaifin jinjiri da maijego a ranar da aka cika kwana bakwai da haihuwar jinjiri. maza sukan taru ne a kofar gida, su kuwa mata suna zama a cikin gida ne domin hidimar shirya abinci ga bakin da suka halarci bukin. A lokacin bukin akan kawo goro a raba shi kasha biyu, wato gefen maigida da gefen mai haihuwa, domin kowa ya raba wa mutanensa da suka zo taya shi murna. Akwai wani kaso da ake kebe wa Malamai masu du‟a‟i da kuma wamzamai da ma'aska da makera su ma da nasu kaso na la'addu. Wannan shi ne ainihin bukin wanda a dalilin rada sunan ne ake shirya taron suna. Duk da yake zamani ya fara yi wa wannan al‟adar rauni domin wasu a masallatai suke yi wa 'ya'yansu addu'ar zanen suna. Ma'ana ba su yin taron suna, sai mata su shirya taron walima a cikin gida daga baya.
Yanka Dabbar Suna da Abincin Gara
[gyara sashe | gyara masomin]- Dabbar suna, dabba ce da akan tanada domin a yanka ta hanya tabbatar wa da jinjiri suna yanka. Galibi a kasar Hausa akan yanka Rago ko Tumaki ko Awaki ko ma a wasu lokuta Shanu a wajen zanen suna. Da zarar an yanka dabbar suna da nufin a sanya suna iri kaza ga jinjin sanya suna iri kaza”
- Wannan abinci ne da ake yi na musamman domin bukukuwan aure ko suna a kasar Hausa. Galibi irin wannan abinci ya shafi masa (waina) da alkaki da da Fanke da cincin da naman kaza da dai sauran su. Akan raba wa mutanen da suka zo shaidar radin sunan domin su ci, kuma su tafi da shi gidajensu.
Tsagar Gado
[gyara sashe | gyara masomin]Wannan tsaga ce da ake yi a tsakanin Hausawa domin a nuna irin kabilar da mutum ya fito daga cikin kasha-kashen Hausawa. Misali, akwai Zamfarawa da Kabawa da Katsinawa da Kanawa da Zazzagawa da sauransu. A bisa al'ada akan yi wa abin da aka haifa tsagar gado ne tun ranar bukin sunansa.
Wasannin Gado a Ranar Suna
[gyara sashe | gyara masomin]Wasanni ne da suka shafi martaba irin gadon gida ko sana'o'in da mutum ya tashi a cikinsu. Misali idan a gidan Mahauta ne akan yi wasan kawan kaho, ku a yi wasa da wuta idan a gidan makera ne da sauransu.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Abdullahi I.S.S (2008). “ Jiya ba Yau Ba: Waiwaye a Kan Alkadun Matakan Rayuwar Maguzawa na Aure da Haihuwa da Mutuwa.”Kundin digiri na uku: Jami‟ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto.
- ↑ Sallau, B. A., “Ciki da Hanyoyin Tanadinsa a Wajen Hausawa a Yau”, Algaita Journal of urrent Research in Hausa Studies, No.5 Vol.1 September, 2008, Department of Nigerian Languages, Bayero University, Kano, Page 163 – 184
- ↑ Sallau, B. A., Magani a Sha a yi Wanka a Buwaya, (2010), ISBN: 978 – 978 – 48604 – 9 – 9, Designed and Printed by M. A. Najiu Professional Printers, No. 3 Kenya Road, Malali, Kaduna.
- ↑ Sallau, B. A., Wanzanci da Sauye-Sauyen Zamani, (2013) ISBN: 978-978-48604-4-4, Printed by Ahmadu Bello University Press Limited, Zaria. Yahaya da Wasu (2001). Darussan Hausa don {ananan Makarantun Sakandare. Zaria. ABU Press